Sama da Mutane Miliyan 30 na cikin Yunwa, Gwamnati Ta Kawo Hanyar Wadatar da Abinci

Sama da Mutane Miliyan 30 na cikin Yunwa, Gwamnati Ta Kawo Hanyar Wadatar da Abinci

  • Ƙididdiga ta nuna cewa miliyoyin yan Najeriya na fama da rashin abinci wanda hakan ke yin illa garesu musamman mata da yara kanana
  • An jingina dalilin fadawa cikin halin ga cire tallafin man fetur da kuma rashin tsaro da ake fama da shi musamman a jihohin Arewa ta yamma
  • Daraktan yada labaran ma'aikatar kasafin kudi da tsare tsaren tattali ya bayyana matakin da suke dauka domin kawo sauki ga yan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An fitar da kididdiga kan yadda al'umma ke fama da ƙarancin abinci a tarayyar Najeriya.

Bincike ya nuna cewa miliyoyin yan Najeriya ne ke fama da ƙarancin abinci wanda hakan ya jefa rayuwarsu cikin matsala.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

Bola Tinubu
Yan Najeriya sama da 31m na fama da yunwa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta fara motsawa domin ganin kawo dauki a kan halin da al'umma ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya miliyan 31.8 na fama da yunwa

Ƙididdigar Cadre Harmonise ta nuna cewa sama da yan Najeriya miliyan 31.8 ne ke fama da ƙarancin abinci.

An tabbatar da cewa an shiga ƙarancin abinci ne saboda tashin farashi wanda cire tallafin man fetur ya haifar a Najeriya.

Dadin dadawa, an tabbatar da cewa matsalar rashin tsaro musamman a wuraren da ake noma ta kara jefa al'umma cikin matsala.

Hanyar kawo karshen yunwa a Najeriya

Rahoton Channels Television ya nuna cewa daraktan yada labaran ma'aikatar kasafin kudi da tsare tsaren tattali ya ce dole a yi kokarin shawo kan matsalar.

Julie Osagie-Jacobs ya bayyana cewa an samar da hanyar yin haɗaka da ma'aikatu masu zaman kansu wajen wadatar da al'ummar Najeriya abinci.

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

Cikin sa'a, Osagie-Jacobs ya tabbatar da cewa waɗanda aka yi haɗaka da su irin kungiyoyin FAO, GAIN, GIZ sun nuna goyon baya dari bisa dari.

An bukaci bude iyakokin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kare hakkin masu sayayya ta kasa ta bukaci gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasar nan domin shigo da abinci.

Mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi da ya bayyana haka a Bauchi ya ce idan ana shigo da abinci ta halastacciyar hanya za a rage yunwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng