Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule da ASUU, an Samu Bayanai

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule da ASUU, an Samu Bayanai

  • Gwamnatin tarayya ta fara neman hanyar hana yajin aikin da ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ke barazanar farawa
  • Gwamnatin ta kira ƙungiyar ASUU domin tattauna ta yadda za a samo hanyoyin dakatar da shirin yajin aikin da suke yi
  • Ana gudanar da taron ne dai a ɗakin taro na ma'aikatar ilmi ta tarayya tsakanin wakilan ASUU da na gwamnatin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara zama da ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) a birnin tarayya Abuja.

Taron na zuwa biyo bayan barazanar da ASUU ta yi ta tsunduma cikin yaji aiki sakamakon gaza biya mata buƙatunta da gwamnatin tarayya ta yi.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

ASUU ta shiga zama da gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da ASUU Hoto: @EmmanuelOsodoke, @NigEducation
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya ta shiga taro da ASUU

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ana gudanar da zaman ne a tsakanin ɓangarorin biyu a ɗakin taro na ma'aikatar ilmi ta tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Biyo bayan barazanar shiga yajin aiki da ASUU ta yi, ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman, yayin wani taron manema labarai na cika shekara ɗaya a ofis, ya ce gwamnati za ta gana da wakilan ƙungiyar ASUU a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Sai dai, ɓangarorin biyu ba su samu zama a ranar Litinin ɗin ba, duk da cewa ba a bayyana dalilan hakan ba.

Menene manufar taron ASUU da gwamnati?

Taron dai na da nufin hana sake yajin aikin gama gari a jami'o'in gwamnati na Najeriya.

Wakilan ƙungiyar ASUU ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Emmanuel Osodeke, sun samu halartar taron, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar da haka.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Ministan ilmi da manyan ma’aikatan ma’aikatar ilimi ta tarayya, suna cikin ɗakin taron.

Sauran ƴan tawagar ASUU akwai tsofaffin shugabannin ASUU, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugabanta, Farfesa Biodun Ogunyemi.

Gwamnati na shirin hana ASUU shiga yajin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta yi duk abin da ya dace wajen hana kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) tsunduma yajin aiki.

Ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka bayan kammala ganawa da shugabannin ƙungiyar ASUU domin sake duba bukatunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng