Kaduna: Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Sama da 200, SEMA Ta Ɗauki Mataki
- Mummunar ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a ƙananan hukumomin Zaria da Sabon Gari da ke jihar Kaduna
- Shugaban hukumar bada agaji SEMA ta Kaduna, ya ce gwamnati ta ɗauki matakai amma mutane suka yi kunnen ƙashi
- An yi kira ga mazauna garuruwan da ake kyautata zaton ruwa zai iya ambaliya su yi haƙuri su tashi su koma wasu wuraren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Shugaban hukumar agajin gaggawa (SEMA) ta jihar Kaduna Dr. Usman Hayatu-Mazadu ya ce ruwa ya cinye gidaje sama da 200 a Zaria da Sabon Gari.
Dr. Usman Mazadu ya ce mummunar ambaliyar da aka yi sakamakon mamakon ruwan sama ta ruguza gidaje aƙalla 200 a ƙananan hukumomin Zaria da Sabon Gari a Kaduna.
Yadda mutane suka ƙi jin shawarar ambaliya
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa duk da hasashen da aka yi da kuma gargaɗi, amma wasu mazauna yankunan da abin ya shafa ba su tashi daga wuraren ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake hira da manema labarai a Kaduna, shugaban SEMA na jihar ya ce kunnen ƙashin da jama'a suka yi ya haddasa yin asarar dukiyoyi.
Ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna ta fara ɗaukar matakan daƙile illolin da ambaliyar ka iya ƙara haifarwa, kamar gyara magudanan ruwa da wayar da kai.
Mazadu ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da ake hasashen za a samu ambaliyar ruwa da su gaggauta tashi daga wurin.
NEMA da gwamnatin Kaduna sun ɗauki matakai
Channels ta rahoto shugaban SEMA na cewa:
"Na zo nan ne a yau don yi muku bayani kan mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a kananan hukumomin Sabon-Gari da Zariya a ranar Litinin.
"Duk da kokarin da muka yi na ganin an shawo kan lamarin, ambaliyar ta yi barna sosai, sama da gidaje 200 suka ruguje.
"Kamar yadda kuka sani tun watanni uku da suka shige hukumar NiMet ta yi haashen haka kuma mun ɗauki matakan da suka dace domin magance ambaliyar."
- Usman Hayatu-Mazadu
Daga nan sai ya bukaci mazauna yankin musamman manoma da su yi amfani da filayen da gwamnati ta ba su domin noma kana su tashi su koma wasu wuraren.
Ambaliya ta yi ɓarna a Kebbi da Neja
Rahotanni sun nuna ambaliyar ruwa ta yi kaca-kaca da amfanin gonakin al'umma a wasu yankuna da ke jihohin Kebbi da Neja.
Hukumar N-HYPPADEC ta miƙa sakon jaje ga waɗanda ibtila'in ya shafa tare da yabawa matakin gwamnatin tarayya na ware N3bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng