Yan Sanda Sun Cika Umarnin Sufeto Janar, An Yi Holin 'Yan Shi'a a Abuja
- Rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana cafke wasu daga cikin 'yan shi'a da ake zargi da hannu wajen kashe jami'anta
- Wannan na zuwa bayan mutuwar jami'an 'yan sanda da wani mai sayar da kayan tireda a arangama tsankanin jami'an da 'yan shi'a
- Tun bayan harin ne babban sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin cafko wadanda ake zargi cikin lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan kasar nan ta yi holin wasu 'yan shi'a da ake zargi na da hannu wajen kisan jami'anta guda biyu da wani mai sayar da kayan shago.
Lamarin ya faru bayan tashin hankali da aka samu tsakanin 'yan kungiyar IMN mabiya darikar Shi'a da yan sanda a makon da ya gabata.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a safiyar Laraba ne rundunar 'yan sandan ta yi holin wasu daga cikin 'yan shi'ar da ake zargi da haddasa fitina a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin mutanen da ake zargin su ne 'yan Shi'ar da su ka tayar da hatsaniyar akwai maza da mata.
Yadda aka kama 'yan Shi'a a Abuja
Jaridar Osun Defender ta wallafa cewa rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama wasu daga cikin 'yan Shi'a bisa taimakon bayanan da jami'anta su ka samu.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka, inda ya ce lamarin ya biyo bayan umarnin da babban Sufeto, Kayode Egbetokun ya bayar.
Yan sanda sun mutu a arangama da 'yan Shi'a
A wani rahoton kun ji cewa an yi asarar rayukan jami'an tsaro biyu bayan arangama tsakanin rundunar 'yan sandan kasar nan da wasu 'yan Shi'a a babban birnin tarayya, Abuja.
Haka kuma jami'an sun harbe wani mai sayar da kayan masarufi yayin da ya ke gudun neman tsira bayan 'yan sandan sun kora wasu daga cikin 'yan Shi'a a Wuse Zone 6.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng