Yajin Aiki: Muhimman Dalilai 5 da Suka Sa ASUU Ta Yi Barazanar Rufe Jami'o'i a Najeriya

Yajin Aiki: Muhimman Dalilai 5 da Suka Sa ASUU Ta Yi Barazanar Rufe Jami'o'i a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Malaman jami’o’in Najeriya karkashin inuwar kungiyar ASUU sun bai gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 ta cika alƙawurra da ta ɗauka ko su shiga yajin aiki.

Ƙungiyar ASUU na shirin rufe jami'o'in gwamnati ne kan wasu alƙawurra da aka mata tun daga 2009 zuwa yanzu kuma ba a aiwatar da su ba.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke.
Wasu daga cikin dalilan ASUU na yin barazanar shiga yajin aiki a Najeriya Hoto: ASUU
Asali: Facebook

Meyasa ASUU ke son yin yajin-aiki?

Shugabannin ASUU sun jima suna kiraye-kiraye da tunatar da gwamnatin tarayya game da yadda za a inganta harkar ilimi amma dai ba wani canji, Tribune ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman buƙatun ASUU da suka shafi fannin ilimi sun haɗa da samar da kudade don farfado da jami'o'in gwamnatin da sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Matakan da aka ɗauka a taron gwamnatin Tinubu da ASUU sun bayyana

Legit Hausa ta tattaro muku muhimman dalilai biyar da suka sa ASUU ta ga ba ta da zaɓi face ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

1. Rashin ware kudin inganta jami'o'i

Ƙungiyar ASUU ta jima tana kokawa kan rashin warewa jami'o'in gwamnati isassun kuɗin da za su tafiyar da harkokin karatu da kayan aiki na zamani.

Har ila yau, ASUU ta koka kan rashin isassun ma'aikata, masaukin dalibai, rashin isassun kayan aikin dakunan gwaje-gwaje da dakunan karatu a jami'o'in Najeriya.

Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban ASUU reshen jami'ar Ibadan, Farfesa Ayoola Akinwole ya nuna damuwa kan ƙarancin kasafin da ake warewa fannin ilimi.

A cewarsa, wannan ne dalilin da makarantu ke fama da matsaloli da dama, kamar rashin kayan aiki na zamani, Punch ta ruwaito.

2. Sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009

ASUU ta bayyana rashin jin dadinta kan jinkirin gwamnati na sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009, ta bar malaman jami'a a tsarin albashi guda sama da shekaru goma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ɗauki mataki na gaba bayan ganawa a Abuja

Malaman jami'o'in sun jima suna rokon gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniyar da ta suka sanyawa hannu a 2009.

Bayan rashin mutunta shawarwarin kwamitoci guda uku a jere, gwamnatin tarayya ta yi wa malaman ƙarin albashin kashi 25% da kashi 35% ba tare da la’akari da tsarin da aka shimfida ba.

3. ASUU ta dage kan batun IPPIS

Duk da umarnin majalisar zartaswa karkashin shugaban ƙasa Bola Tinubu na cire ASUU daga tsarin IPPIS, har yanzu ba ta sauya zani ba, ana biyan malaman jami'a albashi da tsarin.

Lamarin dai ya fusata ASUU, inda ta bayyana cewa ba za ta lamunci a ci gaba da biyan ƴaƴanta albashi da IPPIS ba tun da shugaban ƙasa ya ba da umarnin a cire su.

4. Cin gashin kan jami'o'i

Kungiyar ASUU ta damu da yadda ake neman binne batun ba jami’o’i ‘yancin cin gashin kansu da kuma ƙaruwar jami’o’in barkatai a sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta sanya labule da ASUU, an samu bayanai

A cewar ƙungiyar, hakan ka iya zama barazana ga ingancin ilimin da za a riƙa ba ƴan Najeriya.

5. Alawus da albashin da aka riƙewa malamai

Alawus-alawus da ake biyan malaman jami'o'i da kuma albashin watannin da gwamnati ta riƙe masu na daga cikin batutuwan da suka jawo barazanar yajin aiki.

ASUU dai na bin bashin kuɗin alawus-alawus da suka kai N50bn da kuma albashin wata da watanni.

Gwamnatin tarayya ta kafawa ASUU kwamiti

A wani rahoton kuma gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakan shawo kan kungiyar ASUU bayan ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya.

A taron da suka yi ranar Laraba, gwamnati ta hannun ma'aikatar ilimi ta kafa kwamiti da zai sake nazarin bukatun ASUU.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262