Wutar Lantarki: Gwamnatoci Sun Haɗa N100bn domin Hana Kamfanoni Zaluntar Mutane

Wutar Lantarki: Gwamnatoci Sun Haɗa N100bn domin Hana Kamfanoni Zaluntar Mutane

  • Gwamnatin tarayya da ta jihohi sun hada biliyoyin Nairori domin sayo mitar wuta don rabawa yan kasa
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce za a sayo mitocin domin waɗanda ba su da shi a gidajensu
  • Ministan ya bayyana cewa matakin zai kakkabe yadda kamfanonin rarraba wutar lantarki ke cutar jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta haɗa kai da gwamnatin jihohi wajen samar da Naira Biliyan 100 domin sayo mitoci.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka a ziyarar da ya kai Ibadan da ke jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Adebayo
Gwamnatin Najeriya za ta haɗa gwiwa da jihohi domin sayi mitocin wutar lantarki na N100bn Hoto: Hon. Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ministan ya ce za a sayi mitocin ƙarkashin shirin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu don magance matsalar biyan kudin wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ana sa ran jama'ar ƙasar da ba su da mita za su samu a ƙarkashin shirin domin sauƙaƙa biyan kuɗin lantarki da rage cutar da kamfanonin rarraba wuta ke yi.

"Dalilin rashin biyan kuɗin wuta" - Minista

Gwamnatin tarayya ta ce wasu daga cikin masu amfani da hasken lantarki ba sa biyan kudin wuta saboda wasu dalilai ciki har da rashin yadda da kamfanonin wuta.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce wasu na zargin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki da cutarsu wajen rubuta kuɗi fiye da wutar da su ka sha.

Su wanene ke da mitar wuta?

An gano cewa daga cikin mazauna kasar nan sama da miliyan 12 da ke amfani da lantarki, kusan miliyan biyar ne kawai ke amfani mitocin lantarki.

Kara karanta wannan

Kano: Majalisa ta nemi taimakon Gwamna Abba bayan iftila'in da ya faru a jihar

Adebayo Adelabu ya ce wannan matsala ce babba, ganin yadda ake da kusan mutane miliyan bakwai da ba su da mita.

"An samu karuwar wuta" Adelabu

A baya kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce an samu ƙaruwar hasken wutar lantarki a Najeriya saboda jajircewar Bola Tinubu.

Mista Adelabu ya ce gwamnatin tarayya ta san yadda sauran bangarorin ƙasar nan su ka dogara da wutar lantarki wajen gudanar da ayyukan cigaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.