Bayan Tafiyar Yusuf Bichi, an Bukaci Babban Jami'in Gwamnati Ya Yi Murabus
- An yiwa shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, hannunka mai sanda kan jan ragamar kamfanin
- Wani babban mamba a jam'iyyar PDP, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, ya buƙaci Mele Kyari da ya yi murabus daga kan muƙaminsa
- Abdul-Aziz ya shawarci Mele Kyari da ya yi murabus ɗin ne bayan shugabannin hukumomin DSS da NIA sun ajiye aikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An buƙaci shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya yi murabus daga kan muƙaminsa.
Wani babban mamba a jam'iyyar PDP, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, ya ba shugaban na kamfanin NNPCL shawarar ya ajiye aikinsa.
Abdul'aziz Na'ibi Abubakar ya ba Mele Kyari wannan shawarar ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin DSS, NIA sun yi murabus
Shawarar da ya ba Mele Kyari na zuwa ne bayan shugaban hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi da na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Alhaji Ahmed Rufa'i Abubakar sun yi murabus daga muƙamansu.
Bayan murabus ɗin na su, Shugaba Tinubu ya maye gurbinsu da sababbin waɗanda za su ci gaba da jan ragamar hukumomin.
A hukumar NIA, Shugaba Tinubu ya naɗa Mohammed Mohammed domin maye gurbin Alhaji Ahmed Rufa'i Abubakar.
Adeola Oluwatosin Ajayi zai jagoranci hukumar DSS bayan murabus ɗin da Yusuf Magaji Bichi ya yi a ranar, 24 ga watan Agustan 2024.
Wace shawara aka ba Mele Kyari?
Mamban na PDP ya buƙaci Mele Kyari da ya yi murabus ka da ya bari har sai ta kai ga an kunya ta shi ta hanyar sauke shi daga muƙaminsa.
"Yanzu saura kai, Mele Kyari. Idan kaga dama ka da ka yi murabus, ka jira har sai sun kunya ta ka."
- Abdul-aziz Na'ibi Abubakar
Atiku ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi kira ga Bola Tinubu kan dawo da tallafin man fetur.
Atiku Abubakar ya ce ya kamata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi halin maza wajen fadawa yan Najeriya cewa ya dawo da tallafin mai maimakon boye boye da yake.
Asali: Legit.ng