Tsohon Dan Majalisa Ya Biya Gwamnati Rancen Kudin Karatun da Ya Karba Bayan Shekara 47

Tsohon Dan Majalisa Ya Biya Gwamnati Rancen Kudin Karatun da Ya Karba Bayan Shekara 47

  • Tsohon ɗan majalisar wakilai, Honarabul Lanre Laoshe ya biya rancen da gwamnatin tarayya ta ba shi a lokacin da yake karatunsa
  • Tsohon ɗan majalisar ya biya rancen da ya samu na N1,200 a tsakanin shekarar 1976 zuwa 1979 da N3.1m
  • Hukumar NELFUND wacce ta tabbatar da biyan bashin da tsohon ɗan majalisar ya yi, ta ce ya nuna godiyarsa ga gwamnati bisa taimakon da ta yi masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan majalisar wakilai wanda ya amfana da bashin da gwamnatin tarayya ke ba ɗalibai, ya biya bashin da aka biyo shi.

Honarabul Lanre Laoshe wanda ya samu bashin na N1,200 a tsakanin shekarar 1976 zuwa 1979, ya biya bashin da kuɗi har N3,189,217m.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

Tsohon dan majalisa ya biya NELFUND bashi
Honorabul Lanre Laoshe ya biya bashinɓdaɓya ci shekara 47 da suka wuce Hoto: @NELFUND
Asali: Twitter

Tsohon ɗan majalisa ya biya bashi

Hukumar kula da asusun ba ɗalibai rancen kuɗin karatu (NELFUND) ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, tsohon ɗan majalisar wanda ya amfana da bashin a lokacin karatunsa, ya nuna godiyarsa bisa taimakon da gwamnatin tarayya ta yi masa a lokacin.

Yadda ya gano ƙimar kuɗin a yanzu

Ya bayyana cewa ya samo matsakaicin farashin canjin Dala zuwa Naira daga CBN na shekarun 1972 zuwa 1985 domin gano adadin yawan N1,200 a yanzu.

Bayanan da ya samo sun nuna cewa ana canjin Dala a kan farashin $1.00/N0.596 a shekarar 1979, wanda hakan ke nufin cewa N1,200.00 na daidai da $2,013.42 a lokacin.

Honarabul Lanre Laoshe ya yi amfani da farashin canjin Dala na yanzu na $1.00/N1,583.98, inda ya gano cewa kuɗin a yanzu suna daidai da N3,189,217.00.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An samu matsala a taron da gwamnatin Tinubu za ta ya da ASUU

A bisa hakan sai ya biya bashin ga hukumar NELFUND domin nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya kan rawar da ta taka lokacin da yake yin karatunsa.

NELFUND ta dakatar da ba da rance

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula da asusun ba ɗalibai rancen kudin karatu NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin.

Hukumar ta sanar da dakatarwar wadda za ta dauki tsawon kwanaki 14 biyo bayan karancin daliban manyan makarantun jihohi da ke neman rancen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng