'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 1 Tare da Sace Wasu Mutane a Nasarawa
- Ƴan bindiga sun kai hari a jihar Nasarawa inda suka hallaka wani bawan Allah da bai san hawa ba, bai san sauka ba
- Miyagun ƴan bindigan a yayin harin wanda suka kai a ƙauyen Gabaduke na ƙaramar hukumar Toto, sun yi awon gaba da wasu mutum biyu
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce an tura ƙarin jami'ai domin ceto mutanen
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Ƴan bindiga sun hallaka wani mutum mai suna Garba Yakubu a wani hari da suka kai a jihar Nasarawa.
Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mutum biyu a yayin da suka kai harin a ƙauyen Gabaduke na ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Jaridar Tribune ta rahoto cewa kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kakakin rundunar ƴan sandan, ƴan bindigan sun shiga gidan Agaba Yakubu da daddare, inda suka harbi Garba Yakubu tare da sace wasu mutum biyu, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
"A ranar 25 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 2:00 na dare, DPO na Toto ya samu kiran gaggawa kan shigar ƴan bindiga gidan Agaba Yakubu da ke ƙauyen Gadabuke."
"A yayin harin, an harbe Garba Yakubu tare da yin garkuwa da wasu mutum biyu."
"Biyo bayan samun rahoton, ƴan sanda sun garzaya zuwa wajen inda suka ɗauko gawar marigayin, sannan daga baya suka ba iyalansa domin yi masa Jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada."
- ASP Ramhan Nansel
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa dangane da mutum biyun da aka sace, an tura ƙarin jami'an tsaro zuwa ofishin ƴan sanda naToto domin ceto su daga hannun ƴan bindigan.
Ƴan bindiga sun sace mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun sace sama da mutane 150 tare da yin awon gaba da shanu sama da 1,000 a wasu ƙauyukan da ke masarautar Gobir ta jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun hallaka mai martaba Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa, wanda shi ne Hakimin Gatawa.
Asali: Legit.ng