Ana Zargin Rigima da Ribadu Ya Tilasta Bichi Yin Murabus Daga Shugabancin DSS

Ana Zargin Rigima da Ribadu Ya Tilasta Bichi Yin Murabus Daga Shugabancin DSS

  • Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya sauya daraktan DSS saboda rashin jituwa da Mallam Nuhu Ribadu
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa ana zargin Bichi da kawo cikas wurin tabbatar da dakile yan ta'adda da kuma masu garkuwa
  • Wannan na zuwa ne bayan Yusuf Bichia yi murabus da kuma maye gurbinsa da Adeola Ajayi a jiya Litinin 26 ga watan Agustan 2024 da muke ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana musabbabin shirin korar tsohon daraktan hukumar DSS, Yusuf Bichi da shugaban kasa, Bola Tinubu ke yi.

Wata majiya ta tabbatar da cewa Bichi ya yi murabus ne saboda ba su ga maciji da mai ba da shawara a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Zargin rashin Turanci: An garkame hadimin Sanata Tambuwal kan sukar gwamna

Rigima da Ribadu ka iya zama dalilin cire Bichi daga shugabancin DSS
Ana zargin Bola Tinubu ya cire Bichi daga shugaban DSS saboda sabaninsa da Nuhu Ribadu. Hoto: @abba_yusufbichi, @DOlusegun.
Asali: Twitter

Ana zargin Bichi bai shiri da Ribadu

The Guardian ta ruwaito cewa Tinubu ya na iya sallamar duk wanda ke kawowa Ribadu cikas a kokarin yaki da ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan nadin sabon daraktan hukumar, Adeola Ajayi wanda shi ne ya maye gurbin Mr. Bichi daga mukaminsa.

Tinubu ya sanar da nadin sabon shugaban ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya tabbatar a jiya Litinin 26 ga watan Agustan 2024.

DSS: Tinubu ya yabawa Yusuf Bichi

Shugaba Tinubu ya yabawa Bichi wurin ba da gudunmawa a harkokin tsaro da bankado bayanai inda ya yi masa fatan alheri a rayuwarsa.

"Ribadu na zargin Bichi yana masa katsalandan game da umarnin Bola Tinubu wurin tabbatar da murkushe yan ta'adda da masu garkuwa."

- Cewar majiyar

Yusuf Bichi ya yi murabus daga mukaminsa

Mun baku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS.

Kara karanta wannan

Yusuf Bichi ya yi murabus: Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar DSS

Cif Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 26 ga watan Agustan 2024.

Rahotanni sun tabbatar cewa Bichi, ya yi murabus a jiya Litinin 26 ga watan Agusta da mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasa Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.