Kano: Abba Ya Gabatar da Kasafin Kudi domin karin Albashi da sauran Ayyuka
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da karin kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar domin neman amincewa
- Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Isma'il Falgore ya karanta wasikar da Abba Kabir Yusuf ya tura musu a yayin zaman majalisar
- Haka zalika Isma'il Falgore ya bayyana manyan abubuwan da za su laƙume karin kasafin kudin ciki har da biyan albashi N70,000
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura bukatar amincewa da karin kasafin kudi ga majalisar dokokin jihar Kano.
Kakakin majalisar, Isma'il Falgore ya karanta wasikar da Abba Kabir Yusuf ya tura musu a zaman majalisar.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa karin kasafin kudin da Aban Kabir Yusuf ya tura ya haura Naira biliyan 99.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasafin kudin da Abba ya tura majalisa
Daily Post ta wallafa cewa Abba Kabir Yusuf ya tura buƙatar amincewa da karin kasafin kudi ga majalisar dokokin jihar Kano domin yin ayyukan cigaba.
Shugaban majalisar dokokin jihar, Isma'il Falgore ya bayyana cewa karin kasafin kudin ya haura Naira 99.2 biliyan.
Kasafi zai shafi karin albashi a Kano
Isma'il Falgore ya bayyana cewa karin kasafin kudin zai shafi ayyuka na musamman ciki har da batun karin mafi karancin albashi zuwa N70,000.
Haka zalika Isma'il Falgore ya kara da cewa kasafin zai mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya da walwalar al'umma wanda suna cikin ayyukan da gwamnatin ta saka a gaba.
Dan majalisa ta yi kira ga Abba Kabir
Dan majalisar jiha mai wakiltar Nasarawa ya yi kira ga Abba Kabir Yusuf kan gyara filin wasa da ke unguwar Gawuna.
Yusuf Aliyu ya ce filin wasan ya zama kango da mutane ke shaye shaye da kuma mafaka ga barayi da miyagu.
Karin albashi: Inuwa ya yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta fitar da sanarwar shirin Muhammadu Inuwa Yahaya na fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashin N70,000.
Gwamna watau Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da walwalar ma'aikata a Gombe.
Asali: Legit.ng