Duk da Karancin Abinci a Najeriya, Basarake Ya Umarci Kulle Kasuwanni

Duk da Karancin Abinci a Najeriya, Basarake Ya Umarci Kulle Kasuwanni

  • Duk da halin matsi da karancin abinci a Najeriya, basarake a jihar Ondo ya umarci rufe kasuwanni saboda bikin gargajiya
  • Oba Aladetoyinbo Aladelusi da ke sarautar Akure ya ce an dauki matakin ne saboda muhimmancin bikin ga al'umma
  • Basaraken ya bukaci al'umma musamman mazauna birnin Akure da su tabbatar sun bi umarni tare da bin dokoki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Fitaccen basarake a jihar Ondo ya ba da umarnin rufe kasuwanni saboda gudanar da bikin gargajiya.

Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Aladelusi ya umarci kulle kasuwannin ne a yau Talata 27 ga watan Agustan 2024.

Basarake ya ba da umarnin kulle kasuwanni a yankinsa
Basarake a jihar Ondo ya bukaci kulle kasuwanni saboda bikin gargajiya. Hoto: Oba Aladetoyinbo Aladelusi.
Asali: Facebook

Ondo: Basarake ya umarci rufe kasuwanni

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Daily Trust ta tattaro cewa basaraken ya dauki matakin ne saboda bikin Aheregbe na gargajiya da za a gudanar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana gudanar da bikin Aheregbe ne a kowace shekara a birnin Akure mai cike da tarihi da ke daukar hankulan mutane.

Mai magana da yawun basaraken, Michael Adeyeye ya ce babu wanda za a bari ya bude kasuwa ko shago yayin bikin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ondo: Basarake ya ja kunnen al'umma

Basaraken ya shawarci al'umma musamman mazauna Akure da su bi umarnin tare da bin doka da oda saboda muhimmancin bikin.

Sanarwar ta ce shagunan magani ne kadai ba za a tsauwala musu ba saboda muhimmancinsu wurin kare lafiyar al'umma.

Sannan sanarwar ta ce bikin ba zai dakile mutane daga harkokinsu ba musamman masu ababan hawa da sauran jama'a a gari.

Kara karanta wannan

Zargin rashin Turanci: An garkame hadimin Sanata Tambuwal kan sukar gwamna

Sai dai sakataren yada labaran gwamnan jihar, Ebenezer Adeniyan bai yi martani ba kan matakin da basaraken ya dauka

An bukaci gwamna ya hukunta sarakuna

A wani labarin, kun ji cewa wasu matasa a jihar Ondo sun bukaci Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya hukunta wasu daga cikin sarakuna.

Kungiyar Indigenous Youth Leaders ta bukaci gwamnan ya hukunta sarakuna da ke daurewa masu aikata laifuka gindi a jihar.

Matasan sun bayyana shirinsu na goyon bayan gwamnatin jihar da jami'an tsaro domin yakar masu aikata laifuka daban-daban a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.