Bayan Canza Shugaban DSS, Gwamnati Ta Dura kan Gidajen Mai masu Kara Farashi

Bayan Canza Shugaban DSS, Gwamnati Ta Dura kan Gidajen Mai masu Kara Farashi

  • Hukumar kula da raba man fetur ta kasa, NMDPRA ta fitar da gargadi ga masu gidajen mai da suke kara kudi ba tare da bin ka'ida ba
  • Jami'in NMDPRA ya ce gwamnatin tarayya ba za ta zuba ido ga gidajen mai suna wahalar da yan kasa wajen kara musu farashi ba
  • Kwanaki uku da sanarwar da NMDPRA ta fitar, Legit ta tattauna da wani dan acaba a jihar Gombe domin jin ko labari ya canza

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - hukumar NMDPRA ta fitar da sanarwa mai zafi kan gidajen mai da suke kara farashi a fadin Najeriya.

Kakakin NMDPRA, George Ene-Ita ya ce ba za su zuba ido suna gani ana saka yan Najeriya cikin wahalar mai da gangan ba.

Kara karanta wannan

"Za mu saka kafar wando daya da ku": Majalisar Tarayya ta ja kunnen al'umma

Gidn mai
Gwamnati za ta hukunta gidajen mai masu kara kudi. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa George Ene-Ita ya ce bai kamata farashin litar man fetur ya haura N650 a Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karin kudin man fetur

Wasu masu gidajen mai sun bayyana cewa ba su samun damar sayen mai daga kamfanin NNPCL sai dai ta wajen yan kasuwa.

A saboda haka ne suka ce idan suka saye mai a wajen yan kasuwa farashin na karuwa kuma suma dole su kara farashi.

NMDPRA ta fusata kan farashin mai

Jaridar Tribune ta wallafa cewa kakakin NMDPRA, George Ene-Ita ya ce maganar da yan kasuwar suka yi babu gaskiya a cikinta kwata kwata.

George Ene-Ita ya ce ya fadi haka ne domin suna da masaniya a kan farashin da NNPCL yake ba yan kasuwa man fetur wanda bai kamata a samu wani kari ba.

Gwamnati ta dura kan masu gidajen mai

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

George Ene-Ita ya bayyana cewa a yanzu haka sun fara shirin kulle gidajen mai da suka saka farashi da ya wuce ƙa'ida.

Kakakin ya gargadi duk masu gidajen mai da su nisanci kara farashi kafin NMDPRA ta dura kansu ba sani ba sabo.

Legit ta tattauna da dan acaba

Wani dan acaba a jihar Gombe, Muhammad Ibrahim ya zantawa Legit cewa har yanzu suna sayen man fetur da tsada.

Muhammad ya kara da cewa har yanzu ba a kulle gidajen man da suke kara kudi ba sabanin yadda hukumar NMDPRA ta yi alkawari.

2027: Atiku ya yi magana kan tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sake magana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da tallafin mai.

A maganar da ya yi a wannan karon, Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu na son yin amfani da kuɗin tallafin mai domin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng