"Sanusi II Ne Madubinmu" Sanata Ya Fadi Abin da Ya Kamata Arewa Ta Yi da Hikimominsa
- Sanatan Bauchi ta Arewa, Abdul Ningi ya kwarara yabo da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan irin shugabancinsa
- Sanata Ningi ya ce idan har yankin Arewacin Najeriya ta shirya dakile matsalolinta to dole ta yi amfani da hikimomin Sarkin
- Sanatan ya bayyana haka ne yayin ziyarar Sarkin garin Ningi game da rasuwar Sarki Yunusa Danyaya a ranar Lahadi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sanata Abdul Ningi ya fadi darussan da yan Arewa za su koya daga rayuwar Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Arewa ya ce shawarwarin Sarkin za su taimaka wurin dakile matsalolin Arewacin Najeriya.
Sanata Ningi ya yabawa Sarki Sanusi II
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan Sarkin, Mannir Bayero ya fitar da Punch ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Sanatan ya bayyana haka ne bayan tarbar Sarkin yayin ta'azziyar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya.
Ya ce Sanusi II mutum ne mai ilimi da ya kamata a yi amfani da kwarewarsa wurin tabbatar da dakile matsalolin yankin.
Sanata Ningi ya fadi muhimmancin Sanusi II
"Sanusi II mutum ne mai kima da kuma tarun ilimi wanda ya kamata yankin Arewa ta yi amfani da shi idan ta shirya dakile matsalolinta."
"Duk wasu kabilu da ke Najeriya a yanzu suna godiya da irin gudunmawar da ya bayar ga marasa karfi da kuma tsarin shugabancinsa mai cike da hikima."
"Muna matukar godiya da kuma addu'a ga Sanusi II wanda ke fifita bukatun al'umma fiye da komai a rayuwarsa."
- Sanata Abdul Ningi
Kano: An yi bore bayan tube dagatai
Kun ji cewa mazauna yankin Fangido da Daba da Danbagina da kuma Santolo a jihar Kano sun ki amincewa da korar dagatai 3 a kauyukansu.
Hakimin da ke kula da kauyukan wanda Sarki Sanusi II ya nada shi ya sallami dagatan da ake ganin ya saba ka'ida da kuma doka.
Rahotannin sun tabbatar da cewa Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa ya samu umarni ne daga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusu II.
Asali: Legit.ng