Abin Kunya: Yan Sanda Sun Cafke Malami na Luwaɗi a Masallaci
- Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum, Abubakar Talba yana da ake zargi ya ɗauko almajirai biyu zuwa Bauchi
- Rundunar yan sanda ta zargi Abubakar Talba da aikata laifin luwaɗi da daya daga cikin yaran da ya dauko a matsayin almajiransa
- Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya bayyana matakin doka da za su dauka a kan Abubakar Talba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani matashi bisa zargin aikata laifin luwaɗi da safarar yara ƙanana.
An zargi matashin mai suna Abubakar Talba da dauko yara ƙanana biyu daga jihohin Kano da Katsina zuwa Bauchi.
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a Facebook cewa Abubakar Talba ya dauko yaran ne daga tsangaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga ina malamin ya dauko almajiran?
Bayanan yan sanda sun nuna cewa Abubakar Talba ya dauko yaro na farko ne daga tsangaya a karamar hukumar Fagge a Kano wanda asali ya zo ne daga Kasar Nijar domin karatun allo.
Daga nan kuma sai ya wuce Daura a jihar Katsina inda ya samu yaro na biyu, kuma ya dauko yaran ne a matsayin almajiransa da kuma cewa zai ba su jari su fara kasuwanci.
Malami ya yi luwaɗi a masallaci
Yan sanda sun bayyana cewa kafin zuwa Bauchi ya wuce da yaran zuwa Danbatta a Kano inda ya aka zarge shi da aikata luwaɗi da daya daga cikinsu a masallaci.
Daga nan ne kuma sai Abubakar Talba ya wuce da yaran zuwa Bauchi inda aka zarge shi da cigaba da aikata luwaɗi da yaron kafin yan sanda su kama shi.
Yan sanda sun yi managa kan luwaɗi
Kwamishinan yan sanda a jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya tabbatar da cewa za su mika Abubakar Talba zuwa kotu da zarar sun kammala bincike.
CP Auwal Musa Muhammad ya kuma yi kira ga al'umma da su cigaba da ba yan sanda bayanai domin a samu a cafke miyagu a fadin Najeriya.
An gargadi yan luwadi a Barundi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Burundi ya ja layi kan masu luwadi da auren jinsi inda ya bukaci daukar mummunan mataki a kansu.
Shugaba Evariste Ndayishimiye ya bayyana ce wa duk wanda aka kama da aikata luwadi a kasar Burundi ya kamata a jefe shi a filin wasa.
Asali: Legit.ng