"Ba Allah Ya Kawo Mana Talauci Ba," Tsohon Shugaban Kasa Ya Ja Kunnen Shugabanni

"Ba Allah Ya Kawo Mana Talauci Ba," Tsohon Shugaban Kasa Ya Ja Kunnen Shugabanni

  • Cuf Olusegun Obasanjo ya ce shugabanni da al'umma nahiyar Afirka sun yi barci ta yadda ba su iya amfani da arzikin da Allah ya ba su
  • Tsohon shugaban ƙasar ƴa kuma ja kunnen shugabanni, inda ya ce matuƙar ba a ɗauki matakin gyara ba to matasa dai sun fara zuwa wuya
  • Obasanjo ya ce talaucin da ya yi katutu a Afirka ba daga Allah yake ba, son zuciyar wasu ɗaiɗaiku ne ya jawo fatara a Afirka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kenya - Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce za a samu matsala mai girma idan shugabannin Afirka ba su magance matsalolin da ke addabar matasa ba.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

Cif Obasanjo ya bayyana cewa wannan fatara da talaucin da al'umma ke ciki a nahiyar Afirka ba kaddara ba ce daga Allah, wasu mutane nw suka jawo matsalolin.

Olusegun Obasanjo.
Obasanjo ya bukaci shugabannin Afirka su farka daga magagin barcin da suke yi Hoto: Chief Olusegun Obasanjo
Asali: Getty Images

Olusegun Obasanjo ya bayyana haka ne a wajen bude taron al'adun Afirka FESTAC Africa Festival a filin wasa na Jomo Kenyatta da ke Kisumu a kasar Kenya, Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Talauci ba shi da alaƙa da Afirka'

Tsohon shugaban ƙasar ya ce idan aka duba ɗumbin albarkatun da Allah ya jibge a nahiyar Afirka, babu dalilin da da zai sa talauci ya yiwa mutane katutu.

"Ba dalilin da zai sa talauci ya mamaye Afirka, fatarar da muke ciki ba daga Allah ba ne, rashin tunanin mu ne ya jawo mana talauci amma ba daga Allah ba ne."
"Lokaci ya yi da za mu farka daga barci saboda mu na da ɗumbin arziƙi, idan muka waiwayi tarihi, waɗannan mutanen suna zuwa Afirka ne su kwashi baƙaƙen fata domin su azurta kansu.

Kara karanta wannan

"Muna bukatar taimakonka": Diyar Ado Bayero ta kuma neman alfarmar Abba Kabir

"Safara da kasuwancin bayi ne ya kawo mulkin mallaka, muna zama silar wadatar wasu amma mu muna zama cikin fatara, ya zama dole mu farka daga barci."

- Obasanjo.

Obasanjo ya tabo maganar ƴancin kai

Tsohon shugaban ƙasar ya ce duk da Afirka ta samu 'yancin kai a siyasance amma har yanzu ba ta samu 'yancin kai a fannin tattalin arziki ba.

Obasanjo ya ce Afirka tana da duk wani abu da ake bukata na waɗata amma kuma ya zauna wasu na amfana da albarkatun nahiyar.

Punch ta rahoton tsohon shugaban na cewa:

"Idan ba mu tashi tsaye ba, to tabbatar muna ka ƙaya, matasan mu sun gaji. an kai su bango, babu aikin yi, sun fusata matuka. Ba za su jira ba, idan muka gaza to fa muna cikin matsala."

Lukman ya sake tada hazo kan zaɓen 2027

A wani rahoton kuma Salihu Lukman ya bayyana cewa kwaɗayin mulki ba zai bar shugabannin adawa su taɓuka komai ba a zaben shugaban ƙasa mai zuwa.

Tsohon jigon APC ya ce dukkan manyan jam'iyyun adawa suna fama da rikicin cikin gida da faɗa da juna kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262