Ana Jimamin Kisan Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Yaron Babban Basarake

Ana Jimamin Kisan Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Yaron Babban Basarake

  • An shiga jimami a jihar Legas bayan ƴan bindiga sun hallaka yaron wani basarake mai sarautar Ojomu na Ajiran
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka shi ne a ranar Litinin, 26 ga watan Agustan 2024 a yankin Agungi da ke Lekki
  • Kisan da aka yi wa sarakin ya firgita mutanen da ke rayuwa a wajen, inda wasu mutane suka bar gidajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Hankula sun tashi bayan bindiga sun hallaka yaron babban basarake a jihar Legas.

Ƴan bindigan sun hallaka yaron basaraken mai sarautar Ojomu na Ajiran, Tijani Akinloye, a yankin Agungi da ke Lekki a jihar Legas.

'Yan bindiga sun yi barna a Legas
'Yan bindiga sun hallaka yaron basarake a Legas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka yi kisan

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa an hallaka yaron basaraken ne a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 1 tare da sace wasu mutane a Nasarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ƙara da cewa an hallaka marigayin ne a kan layin Chevron Drive, kusa da babban kantin Ebano.

Jaridar Tribune ta tattaro cewa mutanen wajen sun bar unguwar saboda tashin hankalin da aka shiga sakamakon kisan da aka yiwa yaron basaraken.

Me ƴan sanda suka ce kan kisan?

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin kan lamarin ya bayyana cewa bai samu rahoton kisan ba.

Sai dai, ya yi alƙawarin cewa zai ba da cikakken bayani da zarar ya samu rahoto kan lamarin.

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan bindiga sun sace mutane a Sokoto

Kara karanta wannan

"Ba mu da labari," Ƴan sanda su yi magana kan sace mutane 150 bayan kisan Sarkin Gobir

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun sace sama da mutane 150 tare da yin awon gaba da shanu sama da 1,000 a wasu ƙauyukan da ke masarautar Gobir ta jihar Sokoto.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun hallaka mai martaba Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa, wanda shi ne Hakimin Gatawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng