Tinubu Vs Buhari: Tsohon Jigon APC Ya 'Fadi' Shugaban da Ya Fi Lalata Kasa
- Tsohon jigo a jam'iyyar APC, Salihu Moh. Lukman ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan halin da yan kasa ke ciki
- Ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta fi ta tsohon shugaba Goodluck Jonathan lalacewa, kuma ta Tinubu na kan hanyar wuce ta
- Tsohon jigon ya ce kamata ya yi jama'ar kasar nan su fara shirin maye gurbin Tinubu da wanda zai gyara kasa a 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon jigo a jam'iyyar APC, Salihu Moh Lukman ya ce kowacce gwamnati a Najeriya na fin wacce ta gada lalacewa.
Salihu Moh Lukman, wanda shi ne tsohon mataimakin APC a yankin Arewa maso Yamma ya ce akwai takaici matuka a yadda gwamnatocin ke mulki.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban na ganin gwamnatin Muhammadu Buhari ta fi ta Goodluck Ebele Jonathan lalacewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma yanzu ta gwamnatin Tinubu na hanyar zama gwamnatin da tafi kowacce lalacewa a tarihin Najeriya.
"Babu wani shiri kan Tinubu," Salihu
Tsohon mataimakin shugaban APC reshen Arewa maso Yamma, Salihu Moh Lukman ya bayyana cewa duk da lalacewar gwamnatin Tinubu, ana zaune kara zube.
Ya ce bai ga wata kwakkwarar alama da ke nuni da cewa ana shirin maye gurbin Tinubu da wanda zai iya ceto kasar nan daga kangin da ta ke ciki a 2027 ba.
Wane hali za a shiga bayan Tinubu?
Tsohon shugaban na fargabar rashin tabbas kan sabon shugaban da zai maye gurbin Tinubu ko zai fi gwamnati mai ci yanzu tabarbarewa.
Salihu ya kara da cewa matukar yan siyasa ba su gyara halin ko in kula da su ke da shi ba, yan Najeriya za su kara zabar Tinubu a 2027.
Jonathan vs Tinubu: PDP na shirin 2027
A baya mun kawo labarin cewa wasu kusoshin jam'iyyar PDP na shirin shawo kan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan domin sake tsayawa takara.
Amma jam'iyyar APC ta ce ya yi wuri a fara maganar zaben 2027, amma duk da haka babu mai doke Bola Tinubu a filin zabe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng