Ana tsaka da Maganar Rikicin Yan Shi’a da Yan Sanda, Tarzoma Ta Ƙara Tashi a Abuja

Ana tsaka da Maganar Rikicin Yan Shi’a da Yan Sanda, Tarzoma Ta Ƙara Tashi a Abuja

  • Rikici ya kara barkewa a kasuwar Wuse da ke birnin tarayya Abuja kan shugabanci da ake ƙoƙarin nada mutane
  • Rundunar yan sanda ta isa kasuwar domin kwantar da tarzomar amma duk da haka mutane sun kulle shagunansu a yau
  • Hakan na zuwa ne bayan an samu arangama tsakanin yan sanda da yan kungiyar Shi'a yayin wani tattaki da suka yi a Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rikici ya barke a birnin tarayya Abuja inda yan kasuwa suka fara tashin hankali kan shugabanci.

Rahotanni sun nuna cewa yan kasuwa sun rufe shagunansu a kasuwar a lokacin da rikicin ya barke.

Kara karanta wannan

Sufetan 'yan sanda ya fusata, ya bayar da zazzafan umarni kan yan Shi'a

Abuja
An yi rikici a kasuwar Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an samu rundunar yan sanda ta isa kasuwar domin kawo karshen rikicin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin yan Shi'a da 'yan sanda

A ranar Lahadi aka samu rikici tsakanin yan sanda da yan kungiyar Shi'a a birnin tarayya Abuja yayin da suke tattaki.

An samu hasarar rayuka a ɓangaren yan sanda da bangaren yan Shi'a inda aka ruwaito cewa jami'an yan sanda biyu sun rigamu gidan gaskiya.

Barkewar tarzoma a kasuwar Abuja

Leadership ta wallafa cewa an samu rikici a kasuwar Wuse da ke birnin tarayya Abuja yayin da aka yi yunkurin dawo da wani da aka kora a matsayin manajan kasuwar.

Wani mai suna Usman Kamba a kasuwar ya bayyana cewa an zargi mutumin da ake son nadawa da tayar da tarzoma a kasuwar a kwanakin baya.

'Yan sanda sun isa kasuwar Abuja

Kara karanta wannan

Miyagu za su ga ta kansu, Rundunar yan sanda ta daukarwa yan Najeriya alwashi

A yayin da ake yi yunkurin mayar da mutumin, wasu matasa sun yiwa mutanen da ke kokarin dawo da shi duka kamar yadda wani dan kasuwa ya bayyana.

An ruwaito cewa yan sanda sun isa kasuwar suna kwantar da hankali amma duk da haka mutane sun rufe shaguna sun tafi da misalin karfe 2:00 na rana.

An rufe kasuwa a Abuja bayan rikici

A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja ya rufe kasuwar Dei-dei bayan rikicin da ya barke tsakan yan kasuwa da yan acaba.

Ministan ya ba da umarnin ne bayan ya jagoranci jami’an gwamanti da shugabannin tsaro a ziyarar gani da ido a yankin da rikicin ya faru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng