Garkuwa da Mutane: Likitoci Sun Tafi Yajin Aiki saboda Garkuwa da wata Likita tun 2023

Garkuwa da Mutane: Likitoci Sun Tafi Yajin Aiki saboda Garkuwa da wata Likita tun 2023

  • Kungiyar likitoci ta kasa (NARD) ta sanar da fara yakin aikin gargadi domin nuna adawa da sace wata likita da aka yi jihar Kaduna
  • NARD ta ce za ta yi yajin aikin ne na tsawon mako daya daga nan kuma idan ba a dauki matakin kirki ba za ta tafi sai baba ta gani
  • A makon da ya wuce ne kungiyar ta sanar da gwamnati cewa za ta tafi yajin aiki matukar ba a ƙubutar da likitar daga jeji ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar likitoci ta kasa ta NARD ta bayyana cewa ta shiga yajin aiki domin tura gargaɗi ga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

An shiga jimami, tirela ta markaɗe tsohuwa da jikarta har lahira

NARD ta shiga yajin aikin ne saboda sace wata likita mai sun Ganiyat Papoola da yan bindiga suka yi a jihar Kaduna tun a bara.

Likita
Kungiyar NARD ta shiga yajin aiki kan sace likita. Hoto: Majority World
Asali: Instagram

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban NARD, Dr Dele Abdullahi ya bayyana matakin da za su dauka idan ba a sauraresu ba bayan kammala yajin aikin gargaɗin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gargadi kan sace likita a Abuja

A makon da ya wuce Legit ta ruwaito cewa ministan lafiya na kasa ya tura takardar gargadi ga sufeton yan sanda da Nuhu Ribadu da kungiyar NARD ta rubuta.

Kungiyar NARD ta bukaci gwamnatin tarayya ta sa baki wajen sake Dr Ganiyat Papoola da ta shafe kusan watanni kusan takwas a hannun yan bindiga.

Yaushe likitoci za su fara yajin aiki?

Shugaban kungiyar NARD na kasa, Dr Dele Abdullahi ya bayyana cewa yajin aikin ya fara ne a yau Litinin da misalin karfe 12:00 na safe.

Kara karanta wannan

Ana shirin rufe jami'o'i, Ministan Tinubu ya sanya lokacin haduwa da ASUU

Dr Dele Abdullahi ya kara da cewa sun dauki matakin ne a wani taro da suka yi a ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta.

Yaushe za a gama yajin aikin NARD?

BBC Hausa ta ruwaito cewa Dr Dele Abdullahi ya ce za su yi yajin aikin gargadi ne har na tsawon mako daya domin ganin matakin da gwamnati za ta dauka.

Ya kuma bayyana cewa matukar ba a dauki matakin kubutar da Dr Ganiyat Papoola ba za su tafi yajin aikin sai baba ta gani.

ASUU za ta iya shiga yajin aiki

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta aika sanarwa ga gwamnatin Bola Tinubu cewa za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani.

Kungiyar ASUU ta ce cikin kasa da mako uku masu zuwa za ta garkame dukkanin jami'o'in kasar, kuma ba ta bayyana ranar budewa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng