WAEC da NECO: Gwamnati Ta Hana 'Yan Kasa da Shekaru 18 Tafiya Manyan Makarantu
- Gwamnatin tarayya ta haramtawa dalibai 'yan kasa da shekaru 18 rubuta jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO
- Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana sabon matakin, inda ya bayyana cewa tuni aka mika umarnin ga hukumomin
- Mamman ya kara da cewa har yanzu gwamnati na kan bakarta na cewa dalibai da ke kasa da shekaru 18 ba za su rubuta UTME ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta haramtawa dalibai yan kasa da shekaru 18 daga rubuta jarrabawar kammala sakandare na WAEC da NECO.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka, inda ya ce tuni aka mika umarnin hakan ga hukumomin da ke da alhakin shirya jarrabawar.
The Nation ta wallafa cewa an bar dalibai masu karancin shekaru su rubuta jarrabawar a wannan shekara ta 2024 a matsayin hanyar tunatar da iyaye cewa daga bana an gama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Mamman ya ce gwamnati ta dauki matakan ne domin ci gaban ilimi da gyara tsarin karatu a fadin kasar nan.
An kayyade shekarun jarrabawar gama sakandare
Gwamnatin tarayya ta bayyana kayyade shekarun dalibai da za su rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu da aka fi sani da UTME, Vanguard News ta wallafa wannan.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana cewa daga yanzu babu dalibin da za a bari ya rubuta jarrabawar matukar shekarunsa ba su kai 18.
Matakin na zuwa bayan hana dukkanin daliban da shekarunsu ya gaza 18 daga rubuta jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO.
Gwamnati ta jaddada cewa wannan ba sabuwar doka ba ce, dama can tana nan.
Gwamnati ta gano masu digirin bogi
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gano yan kasar nan kimanin 22, 500 ne ke rike da shaidar kammala karatu na bogi da su ka samo daga jamhuriyyar Togo da Niger.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa yanzu haka gwamnatin na kokarin nemo masu rike da irin wannan takardu domin hukunta su daidai da abin da su ka shuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng