Gwamnan Sokoto Zai Shiga Matsala kan Kisan Sarkin Gobir, Za a Kai Shi Kotun Duniya
- Kungiyoyin matasa a Sokoto sun dauki haramar maka gwamnati a kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya kan kisan Sarkin Gobir
- Jagoran matasan, Sulaiman Shuaibu Shinkafi ya bayyana sharudan da suka ba gwamnatin ta cika a kan lokaci ko kuma su hadu a kotun ICC
- Dr. Sulaiman Shuaibu Shinkafi ya ce kungiyoyin sun dauki matakin ne saboda sakacin gwamantin jihar da ya haifar da kisan sarkin Gobir
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Abubuwa da dama na cigaba da jan hankulan al'umma tun bayan kisan sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.
Kungiyoyin matasa a Sokoto sun zargi gwamnatin jihar da yin sakaci kan kisar Alhaji Isa Muhammad Bawa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyoyin matasan sun yi alwashin maka gwamnatin Sokoto a kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya (ICC).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Gobir: Za a maka gwamna a ICC
Wasu kungiyoyin matasa 18 sun yi taron kwana biyu kan kisar da yan bindiga suka yiwa sarkin Gobir, Alhaji Muhammad Bawa.
Bayan taron, kungiyoyin sun amince da maka gwamnatin Sokoto a kotun ICC ko kuma ta cika sharudan da suka kafa mata.
Sharudan matasa ga gwamnan Sokoto
Kungiyoyin matasan sun bayyana cewa dole gwamnatin Sokoto ta kori kwamishinan tsaro na jihar.
Haka zalika sun bukaci a ba iyalan sarkin Gobir diyya da kuma gwamnatin ta fito ta bayyana matsayarta kan kisan Alhaji Isa Bawa.
Yaushe za a kai gwamnan Sokoto kotu?
Kungiyoyin matasan sun ce sun ba gwamnatin jihar mako biyu ta cika dukkan sharudan da suka gindaya mata ko kuma su hadu a ICC.
Matasan sun ce gwamnatin Sokoto ce ta gayyaci Sarkin taro amma ta yi sakaci wajen kare rayuwarsa a hannun miyagu.
Miyetti Allah ta yi maganar kisan Sarkin Gobir
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Miyetti Allah ta yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa a jihar Sokoto da yan bindiga suka yi.
Kungiyar ta nesanta kanta da duk wasu ayyukan yan bindiga inda ta ce ba ta tare da duk wani ta'addanci da ake yi a fadin kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng