Wani Jirgi da Ya ɗauko Fasinjoji 15 Ya Gamu da hatsari a Najeriya, An Rasa Rai

Wani Jirgi da Ya ɗauko Fasinjoji 15 Ya Gamu da hatsari a Najeriya, An Rasa Rai

  • Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wani jirgin ruwa ya yi haɗari a ƙarshen makon nan a jihar Bayelsa
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ya ɗauko fasinjoji 15 daga Yenagoa zuwa Oporoma
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Bayelsa ya ce har yanzun babu wanda ya kai masu rahoton abin da ya afku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a lokacin da wani jirgin ruwa ya nutse a ƙauyen Okubie da ke ƙaramar hukumar Kudancin Ijaw a jihar Bayelsa.

Bayanai sun nuna cewa jirgin ruwan ya ɗauko fasinjoji 15 kuma ya gamu da hatsari ne a lokacin da ya keto da gudun da ake ganin ya wuce ƙima.

Kara karanta wannan

Kisan Sarkin Gobir ya harzuƙa Gwamnatin Tinubu, minista ya ba sojoji umarnin gaggawa

Taswirar jihar Bayelsa.
Hadarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum ɗaya a jihar Bayelsa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bayelsa: Yadda jirgin ruwa ya yi haɗari

Wata majiya mai tushe daga kauyen ta shaida wa Daily Trust cewa Kwale-Kwalen ya ɗauko fasinjoji ne daga Yenagoa, babban birnin Bayelsa zuwa Oporoma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen yankin da suka iya iyo a ruwa sun yi nasarar ceto dukkan fasinjojin sai mutum ɗaya da ajali ya riske shi.

A cewarsa, mutumin ya mutu ne kafin a zo cetonsa saboda ruwan ya yi masa yawa kuma dai lamarin ya zo da ƙarar kwana.

Me ya jawo hatsarin jirgin?

Ba a gano musabbabin haɗarin jirgin ba har ya zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoton.

Shugaban kungiyar ma’aikatan ruwa a yankin Mista Ipgansi Ogoniba, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ogoniba ya bayyana cewa jirgin ruwan ya yi hatsari ne da yammacin ranar Asabar da ta gabata, 24 ga watan Agusta, 2024, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Kano: Wani Jirgi ɗauke da fasinjoji ya gamu da mummunan hatsari, an rasa rayuka

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, ASP Musa Muhammed, ya ce har yanzu ba su samu rahoton abin da ya faru ba.

Zanga-zanga: Kotu ta amince da bukatar IGP

A wani rahoton kuma kotu ta amince da bukatar ƴan sanda su ci gaba da tsare yara da matasan da aka kama a lokacin zanga zanga na tsawon watanni biyu

Tun farko lauyan sufetan ƴan sanda, Ibrahim Mohammed, ya buƙaci kotun ta ba da damar ci gaba da tsare masu zanga-zangar kafin a gama bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262