'Yan Bindiga Sun Ci Gaba da Ta'addanci a Sokoto Bayan Kisan Sarkin Gobir

'Yan Bindiga Sun Ci Gaba da Ta'addanci a Sokoto Bayan Kisan Sarkin Gobir

  • Miyagun ƴan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare a ƙauyukan ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da sama da mutane 150 tare da sace shanu sama da 1000 a hare-haren da suka kai bayan kisan Sarkin Gobir
  • Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni ya tabbatar da hare-haren da ƴan bindigan suka kai a ƙauyukan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun sace sama da mutane 150 tare da yin awon gaba da shanu sama da 1,000 a wasu ƙauyukan da ke masarautar Gobir ta jihar Sokoto.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun hallaka mai martaba Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa, wanda shi ne Hakimin Gatawa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan Sarkin Gobir, 'yan bindiga sun hallaka yaron babban basarake

'Yan bindiga sun sace mutane a Sokoto
'Yan bindiga sun sace mutane sama da 150 a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni (Arewa) Aminu Boza ya ce an tabbatar da sace mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace mutanen

Aminu Boza ya ce an sace mutane 151 a tsakanin ƙauyen Tsamaye da Sabon Birni.

"Kwana ɗaya da rasuwar Sarkin Gobir, ƴan bindigan sun sake kai hari ƙauyen Tsamaye, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ba a san adadinsu ba."
"Haka kuma sun kai hari ƙauyen Yanfaruna inda suka yi awon gaba da mutane 22 sannan suka je ƙauye na gaba suka yi awon gaba da mutane 11."
"Saboda haka, an yi garkuwa da mutane 192 kuma har yanzu suna tsare a hannun ƴan bindigan."

- Aminu Boza

Jami'an tsaro sun yi ƙaranci

Aminu Boza ya yi zargin cewa babu jami’an tsaro a galibin wuraren da ƴan bindigan ke ta'addancinsu a Sabon Birni, waɗanda suka haɗa da Kwanar Maharba, Turtsawa, Unguwar Lalle, Tagirke da Kwanar Tambazawa.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya maida martani bayan ɗan Sarkin Gobir ya faɗi wanda ya sa a kashe babansu

"An san wuraren da akasarin shugabannin ƴan bindigan nan suke. Misali Bello Turji yana zaune ne a Fakai kuma daga Fakai zuwa Shinkafi nisan bai wuce kilomita uku ba. Halilu yana zaune a ƙauyen Tsububu sai Jummo Baki a ƙauyen Gangara."

- Aminu Boza

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, SP Ahmad Rufa'i, kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa a hukumance ba a kawo musu rahoton sace mutanen ba.

SP Ahmad Rufa'i wanda ya tabbatar da cewa ana sace-sacen mutane a ƙaramar hukumar Sabon Birni, ya nuna cewa da wuya ƴan sanda ke samun irin waɗannan labaran saboda ƙauyukan sun yi nisa.

Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kuɓutar da mutane 30 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile hare-haren ƴan bindiga da dama a wurare daban-daban a jihar.

Kara karanta wannan

Boko Haram zuwa 'yan bindiga: Manyan sarakuna 3 da 'yan ta'adda suka hallaka a Najeriya

Jami’an ƴan sanda sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Dutsinma tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng