Bello Matawalle Ya Gwangwaje Mambobin APC a Zamfara da Abin Arziki
- Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya gwangwaje mambobin jam'iyyar APC a jihar Zamfara da sha tara ta arziƙi
- Tsohon gwamnan na Zamfara ya ba da takin zamani tirela 15 domin rabawa ga ƴaƴan jam'iyyar a faɗin jihar
- Takin zamanin da ƙaramin ministan na tsaron ya ba da za a raba shi ne kyauta ga waɗanda za su ci gajiyarsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya bayar da tallafin tireloli 15 na takin zamani ga mambobin jam’iyyar APC na jihar Zamfara.
Tallafin takin da ministan ya bayar, wanda shugaban jam’iyyar APC reshen jihar,Tukur Umar Danfulani, ya ba sakataren jam'iyyar, ya ce za a raba shi ne faɗin jihar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya rabawa ƴan APC taki
Sanarwar ta ce matakin na ministan zai bunƙasa ayyukan noma, tattalin arziƙi, da ci gaba a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware wani bangare na takin ne ga ministan, kuma ya sayi ƙarin tireloli domin rabawa ta yadda za a samu amfani mai yawa a wannan daminar.
Ya kuma bayyana cewa za a raba dukkanin tireloli 15 kyauta ga waɗanda za su ci gajiyar tallafin da nufin tallafawa manoma.
Tukur Umar Danfulani ya yabawa Bello Matawalle saboda wannan abin arziƙin da ya yiwa ƴaƴan jam'iyyar.
Ya bayyana cewa za a raba takin ne ga mambobin jam'iyyar da ke faɗin mazaɓu 147 a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Matawalle ya ba da tallafi a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayar da tallafin kuɗi N20m ga mutanen da bala’in ambaliyar ruwa da ya shafa a jihar Zamfara.
Bello Matawalle ya bayar da tallafin ne a ranar Talata sakamakon ambaliyar da ta auku a garin Gummi na jihar a ranar Juma'a, 16 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng