Tinubu Ba Ya Najeriya, Sabuwar Matsala Ta Kunno a Bankin CBN
- Tsofaffin ma'aikatan da aka kora daga babban bankin Najeriya (CBN) sun garzaya kotu domin neman a biya su haƙƙoƙin su
- Korarrun ma'aikatan sun shigar da bankin CBN ƙarar ne domin neman a biya su diyya kan korar da aka yi musu daga aiki
- Tsofaffin ma'aikatan na neman kotu ta sanya bankin ya biya su albashin su, alawus-alawus da sauran kuɗaɗen da ya kamata su samu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sama da tsofaffin ma'aikatan babban bankin Najeriya (CBN) mutum 100 suka shigar da bankin ƙara a gaban kotu.
Ma'aikatan sun shigar da bankin CBN ƙara ne a gaban kotun ma'aikata ta ƙasa domin neman a biya su diyya kan korar da aka yi musu daga aiki.
Masu shigar da ƙarar sun bayyana cewa korar da aka yi musu duk da cewa suna da ragowar shekarun aiki, babu adalci a cikinta, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me korarrun ma'aikatan suke nema?
Tsofaffin ma'aikatan suna buƙatar a biya su ragowar albashinsu, alawus-alawus da sauran kuɗaɗen ya kamata su samu, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Lauyan tsofaffin ma'aikatan, Mista Ola Olanipekun (SAN), ya bayyana cewa sun shigar da ƙarar ne domin neman a yi musu adalci ta hanyar sauraron kokensu.
"Korar da CBN ya yiwa waɗanda na ke karewa ba bisa ƙa'ida ba, ta jawo asarar miliyoyin naira a gare su."
"Muna buƙatar kotu da ta tabbatar da cewa CBN ya biya su dukkanin albashinsu, alawus-alawus da sauran kuɗaɗen da ya kamata su samu."
- Mista Ola Olanipekun
Me yasa aka kai CBN ƙara a kotu?
Shigar da ƙarar dai ta biyo bayan matakin da babban bankin na CBN ya ɗauka a watan Mayun 2024 na korar ma'aikata kusan 200 a ƙoƙarin yiwa bankin garambawul.
Korarrun ma'aikatan waɗanda da yawa daga cikinsu suna da sauran shekaru kafin su ajiye aiki, yanzu suna ƙalubalantar korar CBN ya yi musu.
SERAP ta maka CBN ƙara a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta maka babban bankin Najeriya (CBN) ƙara a bisa zargin gaza yin bayanin inda sama da N100bn na yagaggun kuɗi suka yi.
SERAP ta ce tana kuma ɗaukar matakin shari’a a kan CBN saboda N12bn da aka warewa ofisoshin babban bankin a Abeokuta, jihar Ogun, da kuma Dutse a jihar Jigawa.
Asali: Legit.ng