Ana Zargin Jami’an SSS Sun Cafke Fitaccen Dan Jaridan Najeriya, Bayanai Sun Fito

Ana Zargin Jami’an SSS Sun Cafke Fitaccen Dan Jaridan Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) sun cafke fitaccen dan jaridan Najeriya, Adejuwon Soyinka
  • Ana zargin SSS ta tsare dan jaridan bayan cafke shi a a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas lokacin da ya sauka daga Birtaniya
  • Sai dai har zuwa yanzu, hukumar SSS ba ta fitar da wani rahoto kan kama dan jaridar ba, yayin da duk wani kokari na tuntubarsa ya ci tura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar tsaro ta farin kaya ta cafke wani dan jaridan Najeriya, Adejuwon Soyinka, wanda shine editan shiyyar Afirka ta Yamma na jaridar Conversation Africa.

Jami’an SSS sun tsare Mista Soyinka, tsohon editan farko na sashen Pidgin na BBC, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Kara karanta wannan

Kama jiragen Najeriya: An bukaci DSS ta yi gaggawar kama tsohon gwamnan APC

Ana fargabar jami'an tsaron Najeriya sun cafke fitaccen jan jarida, Adejuwon Soyinka
Ana zargin SSS sun cafke fitaccen dan jaridan Najeriya, Adejuwon Soyinka. Hoto: @adejuwonsoyinka
Asali: Twitter

SSS ta cafke dan jaridan Najeriya

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an tsare Mista Soyinka ne da misalin karfe 5:40 na safiyar Lahadi bayan ya taso daga Birtaniya ta jirgin Virgin Atlantic.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ya zuwa wannan rahoton, babu wani dalili da hukumar tsaron ta bayar na tsare fitaccen dan jaridan.

Abokan aikin dan jaridan da ya lashe kyaututtuka kan kwazonsa sun ce sun gaza samunsa saboda ba a daga kira da mayar da sakonni da aka yi masa.

DSS ne suka cafke Adejuwon Soyinka

Sai dai kuma, wani rahoto da jaridar Punch ta fitar, ya nuna cewa jami'an hukumar DSS ne suka kama Adejuwon Soyinka, ba wai jami'an SSS ba.

Jaridar ta ce ta karbi wani sako daga daya daga cikin abokan aikin dan jaridar, wanda ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Dan uwan Kwankwaso ya gaza cika sharadin beli, PCACC ta ci gaba da tsare shi

"Jami’an DSS sun kama Adejuwon Soyinka tare da tsare shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:40 na safiyar Lahadi, 25 ga watan Agusta, 2024"

Da aka tuntubi mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce shi bai san da kama Soyinka ba.

An sace dan jarida a Ribas

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dan jaridan gidan talabijin na Channels da ke aiki a jihar Ribas, Joshua Rogers.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da Rogers a kusa da gidansa da ke Rumuosi a Fatakwal zuwa wani wuri da ba a san ko ina bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.