Matasan da Aka Kama Lokacin Zanga Zanga Sun Shiga Matsala, Kotu Ta Yanke Hukunci

Matasan da Aka Kama Lokacin Zanga Zanga Sun Shiga Matsala, Kotu Ta Yanke Hukunci

  • Kotu ta amince da bukatar ƴan sanda su ci gaba da tsare yara da matasan da aka kama a lokacin zanga zanga na tsawon watanni biyu
  • Tun farko lauyan sufetan ƴan sanda, Ibrahim Mohammed, ya buƙaci kotun ta ba da damar ci gaba da tsare masu zanga-zangar kafin a gama bincike
  • Mai shari'a Emeka Nwite ya kuma ba da umarnin a tsare ƙananan yara daga cikin waɗanda ake zargin a ɓangaren yara na gidan yari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta amince da bukatar da ‘yan sanda suka shigar ta neman tsare masu zanga-zanga 124 da aka kama har na tsawon kwanaki 60.

Kara karanta wannan

Miyagu za su ga ta kansu, Rundunar yan sanda ta daukarwa yan Najeriya alwashi

Kotun ta sahalewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta ci gaba da tsare matasan da aka kama lokacin zanga-zanga na tsawon watanni biyu har sai an gama bincike.

Masu zanga zanga da ƴan sanda.
Kotu ta Amince ƴan sanda su tsare masu zanga-zangar da aka kama a Najeriya Hoto: Nigeria Police
Asali: Twitter

Mai shari'a Emeka Nwite ne ya yanke wannan hukuncin kan bukatar da lauyan sufetan ƴan sanda na ƙasa, Ibrahim Mohammed ya shigar, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace bukata IGP ya shigar kotu

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode Egbetokun ta hannun lauyansa ya roƙi kotun ta ba rundunar ƴan sanda watanni biyu domin ta gama bincike kan laifukan da ake zargi masu zanga-zangar.

Mai shari’a Nwite ya kuma ba da umarnin a tsare ƙananan yara daga cikin waɗanda ake zargin a gidan yarin yara gabanin ƴan sanda su kammala bincike.

Tun farko dai shugaban ƴan sanda ya shigar da ƙarar yara da matasan da aka kama a lokacin zanga-zanga waɗanda shekarun ba su wuce 14 zuwa 34 ba a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun nuna bajintarsu, an gano yadda aka kashe fitinannen dan ta'adda

Wane laifuka ake tuhumar masu zanga-zanga?

Ana zarginsu da aikata laifukan da suka ƙunshi taimakawa ta'addanci, cin amanar kasa, yiwa ƙasa zagon ƙasa, kone kone-kone da ta'addanci.

Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa waɗannan laifuka sun saɓa wa kundin tsarin dokokin hana aikata miyagun laifuka a Najeriya.

Bayan ya umarci a kai ƙananan yara gidan yarin yara, alkalin babbbar kotun ya ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Oktoba, rahoton Vanguard.

Jami'an tsaro sun ceto ɗaliban likitanci

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ceto ɗalibai likitoci 20 waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a makon da ya shige.

Majiyoyi sun bayyana cewa jami'an tsaro da suka kunshi ƴan sanda, sojoji da DSS ne suka kai samame kuma Allah ya ba su nasara a Benuwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262