An samu ci gaba: Kwaleji a Najeriya ta kirkiri abin hawa mai amfani da lantarki
- Wata kwalejin fasaha a jihar Ogun ta samar da adaidaita sahu mai amfani da lantarki, ta bayyana babbar bukatarta
- Masu gudanar da kwalejin sun hango cewa, akwai yiwuwar wannan babban aiki ya rage zaman banza a kasa
- Najeriya na daga kasashen da ke yawan shigo da kayayyakin kasashen waje, ciki har da ababen hawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Ogun - A ranar Juma’ar da ta gabata ne Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Ilaro a Jihar Ogun, Dokta Mukail Akinde, ya ce cibiyar na shirin samar da karamar cibiyar hade-hade da za ta ke kera sabon adaitaita-sahu mai amfani lantarki.
Akinde ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma kamfanoni musamman a bangaren masana’antu da su taimaka wajen ganin an tabbatar da wannan cibiyar kere-kere.
Shugaban hukumar ya ce nasarar samar da babur din zai taimaka matuka wajen rage shigo da kayayyaki daga kasashen waje, rahoton Punch.
Kiran adaidaita sahu mai kafa uku zai rage zaman banza
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ya ce hakan zai rage zaman banza tare da samar da guraben ayyukan yi ga matasan Najeriya da ke kammala karatu babu ayyukan yi.
Akinde ya bayyana hakan ne a lokacin da majalisar gudanarwar cibiyar karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Garba Gashua tare da majalisar kula da kere-kere a wata ziyara da ya kai don ganin sabon kiran.
An ce kwalejin ce cibiyar farko da ta samar da wannan nau'in babur mai amfani da lantarki, wanda aka kera tare da hada shi a cibiyar kirkire-kirkire na kwalejin.
Kiran da ake ga gwamnatin tarayya
Shugaban cibiyar ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara zuba kudade a wannan ma’aikata domin habaka ayyukan kirkiro sabbin abubuwa, bincike da kuma ci gaba.
Najeriya dai na daga cikin kasashen da suka dogara da shigo kayayyaki daga kasashen waje, ciki har da kayayyakin da suka shafi abubuwan hawa.
An sha kira ga gwamnatin kasar da ta tabbatar da samar da hanyoyin kirkira don rage shigo da kayayyakin kasashen waje.
ABU ta kirkiri mota
A wani labarin na daban, Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria ya ce, nan ba da jimawa za ta kera mota ‘yar Najeriya kuma mai amfani da ruwa a madadin fetur.
Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban tsangayar injiniyanci na jami’ar, Farfesa Ibrahim Dabo a ranar Asabar 4 ga watan Maris yayin da bikin ranar injiniyanci ta duniya da aka yi.
Dabo ya bayyana cewa, akwai hobbasa da da yawa jami’ar ta ABU ke yi, ciki har da kera mota mai amfani da wutar lantarki da kuma motoci mai saukaka dumamar yanayi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng