Gwamnan PDP Ya Fadi Abin da Ya Hana Shi Biyan N70,000 bayan Fintiri Ya Biya Ma’aikata

Gwamnan PDP Ya Fadi Abin da Ya Hana Shi Biyan N70,000 bayan Fintiri Ya Biya Ma’aikata

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan fara biyan mafi karancin albashi ga ma'aikata saboda inganta ayyukansu
  • Gwamna Fubara ya ce jiharsa za ta zama ta farko da za ta fara biyan mafi karancin albashin da zarar Gwamnatin Tarayya ta fitar da tsare-tsare
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ya fara biyan mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikatan jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya shirya biyan mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikatan jiharsa.

Gwamna Fubara ya ce yana jiran tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya kan mafi karancin albashin domin fara biyan ma'aikata a jihar.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Malamin Musulunci ya yi zargin za a hada al'ummar Arewa fada, ya yi gargadi

Gwamna PDP ya shirya fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata
Gwamna Siminalayi Fubara ya shirya fara biyan N70,000 ga ma'aikatan Rivers. Hoto: Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Fubara ya shirya fara biyan albashin N70,000

Fubara ya bayyana haka ne yayin gudanar da bikin ma'aikatan jihar na mako da aka saba yi a birnin Port Harcourt da ke jihar, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce jihar ita za ta fara biyan mafi karancin albashin da zarar Gwamnatin Tarayya ta fitar da tsare-tsare kan sabon albashin, PM News ta tattaro.

Hakan ya biyo bayan amincewa da mafi ƙarancin albashin N70,000 domin inganta rayuwar ma'aikata da Bola Tinubu ya yi.

Rivers: Fubara zai inganta rayuwar ma'aikata

Fubara ya ce ma'aikata sune ginshikin cigaban duk wata gwamnati wurin ba da gudunmawa da kwarewarsu domin inganta al'umma baki daya, PM News ta tattaro.

Har ila yau, Fubara ya ce gwamnatinsa ta kara yawan kudi inda ta ke biyan N2bn daga N1bn a kowane wata domin rage basukan yan fasho da kuma giratuti a jihar.

Kara karanta wannan

"Ka da ka bata mana suna": Gwamnonin PDP sun soki Tinubu kan tallafi, sun ba da shawara

Adamawa: Fintiri ya fara biyan albashin N70,000

Kun ji cewa Gwamnatin Adamawa da ke Arewa maso Gabas ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya ɗauka a makon jiya cewa zai fara biyan ma'aikata sabon albashin a ƙarshen watan Agusta.

Shugaban NLC na jihar, Kwamared Emmanuel Fashe ne ya sanar da haka jim kadan baƊ suyan ganawa da gwamnan a Yola na jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.