A Kai Zuciya Nesa: Matashi Ya Yi Yunkurin Aikata Sheke-Kai Bayan Bashi Ya Masa Katutu
- ‘Yan sandan jihar Anambra sun ceto wani matashi daga aikata sheke-kai bayan bashi ya masa katutu
- Rahoto ya bayyana dalilin da yasa matashin ya shiga tashin hankali har ya kai ga daukar mummunan mataki
- Ba wannan ne karon farko da ake samun matasa na daukan munanan matakin da ke kai wa ga rasa rai ba
Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce ta ceto wani matashi mai shekaru 27, Alozie John daga yunkurin kawo karshen rayuwarsa a unguwar Umunnachi da ke karamar hukumar Dunukofia.
Matashin makiyayi dan asalin Isielu ta jihar Ebonyi an ce ya yi yunkurin sheke kansa ne bayan da ya dabaibaye kansa da bashin N1.2m.
Yadda aka gano zai yi sheke-kai
A wata sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Asabar ta bakin mai magana da yawun hukumar, SP Tochukwu Ikenga ta ce, an kai ga ceto shi bayan ganin wata hirarsa ta manhajar WhatsApp.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Ikenga:
“A ranar 23 ga watan Agusta, rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ceto wani matashin da ya yi yunkurin yin sheke-kai. An ceto shi, an ba shi agajin maganin gaggawa kana an ajiye shi a wuri killatacce don zuba masa ido.”
Kasuwar kajin gona sun tunzura matashi
A cewar rundunar, bashi ne ya dabaibaye matashin, wanda aka ce ana binsa kusan N1.2m na kaji da yake kasuwanci da kiwonsu, Punch ta ruwaito.
A halin da ake ciki, tuni rundunar ta kira mahaifiyar matashin, kuma an ce tana ba da hadin kai wajen tabbatar da an kai ga tushen bincike.
Halin da matashin ke ciki a yanzu
Hakazalika, an ce an ajiye matashin a wuri mai aminci tare da zuba masa ido don tabbatar da bai kuma aiwatar da wani nau’in cutar da jiki ba, rahoton Vanguard.
Da kansa, matashin ya ce yana harkallar kaji ne kuma ya sha guba amma bai samu nasarar sadawa ga ubangijinsa ba.
Wata aika-aikar da tsageru suka aikata
A wani labarin, akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai kauyukan Mandung-Mushu da Kopnanle na karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
Rahoton da muka samo ya ce, an fara kai harin ne da misalin karfe 10 na daren Juma’a bayan mutanen kauyen suka gama harkokinsu na rana suka shiga bacci da dare.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa, harin ya haifar da tashin hankali a cikin garin na Bokkos da kewaye.
Asali: Legit.ng