Ceto Daliban Likitoci: 'Yan Sanda Sun Bayyana Kudin Fansan da Aka Biya 'Yan Bindiga
- Rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi maganan kan ɗaliban likitoci da aka samu nasarar cetowa a jihar Benue bayan ƴan bindiga sun sace su
- Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa an ceto ɗaliban ne ba tare da biyan ko sisi a matsayin kuɗin fansa ba
- Muyiwa Adejobi a cikin wata sanarwa da ya fitar ya musanta cewa sai da aka ba ƴan bindigan kuɗin fansa kafin a ceto ɗaliban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da samun nasarar ceto ɗaliban likitoci 20 da aka yi garkuwa da su a jihar Benue.
Ɗaliban waɗanda aka tsare su a dajin Ntunkun da ke ƙaramar hukumar Ado ta jihar, an ceto su ne ba tare da biyan ko sisi a matsayin kuɗin fansa ba.
An ceto ɗalibai a Benue
Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikin ceto ɗaliban wanda ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya gudanar, ya haɗa da yin amfani da jirage guda uku masu saukar ungulu.
A yayin ceto ɗaliban, an cafke mutane da dama da ake zargi yayin da aka hallaka wasu daga cikinsu.
Ɗaliban likitocin waɗanɗa suka haɗa da wasu likitoci, an yi garkuwa da su ne a ranar, 15 ga watan Agusta yayin da suke kan hanyar zuwa wani taro.
Kuɗin fansa nawa aka ba ƴan bindiga?
Sanarwar ta jaddada cewa ba a biya kuɗin fansa ba kafin a samu nasarar ceto ɗaliban daga hannun ƴan bindiga, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
"Saɓanin wasu raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa an biya kuɗin fansa, ko sisi ba a biya ba kafin a sako su. An ceto su ta hanyar nuna ƙwarewa da dabara."
"Muna yabawa hukumomin tsaro, mazauna yankin, da kuma ONSA bisa jajircewarsu da juriyarsu."
- Muyiwa Adejobi
Ƴan sanda sun daƙile hare-haren ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kuɓutar da mutane 30 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile hare-haren ƴan bindiga da dama a wurare daban-daban a jihar.
Jami’an ƴan sanda sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Dutsinma tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47.
Asali: Legit.ng