An Tabo ’Yan Baiwa: Ana Ta Batun Dogs, Masanin Crypto Ya Hango Makomar Tapswap

An Tabo ’Yan Baiwa: Ana Ta Batun Dogs, Masanin Crypto Ya Hango Makomar Tapswap

  • Wani dan Najeriya ya hango cewa, wadanda suka yi tururuwa zuwa fara ‘mining’ kudaden intanet irinsu Tapswap ba lallai su samo komai na riba ba
  • Duk da ya bayyana jin dadi da yadda ‘yan Najeriya ke rungumar fasahar, ya ce ya kamata a kula a kuma yi taka-tsan-tsan wajen neman kudi ta yanar gizo
  • Masanin hakar kudaden intanet, Obani Ebenezer Nwokoma ya bayyanawa Legit irin kura-kuran da ‘yan Najeriya za su kiyaye don su samu alheri a tsarin kudaden intanet irin Tapswap

Najeriya - Fara hakar kudaden intanet na Tapswap ya zo ne jim kadan bayan fashewar Notcoin, inda wasu suka samu ‘yan kudade daga fasahar.

A Najeriya, an ga dandazon jama’a na haba-haba da hakar kudaden intanet na Tapswap a manhajar Telegram, sai dai ana musu hangen ba za su samu komai ba.

Kara karanta wannan

"Muna bukatar taimakonka": Diyar Ado Bayero ta kuma neman alfarmar Abba Kabir

'Yan baiwa za su sha mamaki kan kudin intanet
Makomar kudaden intanet da ake haka ta Telegram | Hoto: Luis Alvarez, TikTok/@tapswap_mining, @iam_safeee
Asali: Getty Images

A wani rubutu da Michael ya yi a kafar Facebook, ya ce wadanda suka kirkiro Tapswap basu da wata masani mai zurfi game da yadda tsarin kudaden intanet ke aiki, musamman wajen asusun ajiya da hanyar shigarsa.

Akwai yiwuwar a rasa komai na Tapswap

Ya kuma kara da cewa, nan ba da jimawa ba masu tara Tapswap za su gaza samun komai saboda ba komai bane a tsarin illa zunzurun damfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani masanin kudin intanet na daban, Obani Ebenezer Nwokoma ya shaidawa Legit cewa, akwai abubuwa da yawa da ka iya jawo masu tara Tapswap ba za su sami komai ba.

Ya shawarci masu amfani da ‘Autoclicker’ da su takaita amfani da shi domin hakan zai iya hana su sami komai ko da kuwa ta tabbata za su samu wani abun.

Kara karanta wannan

Alkali ta yi afuwa ga fursunoni 44, ta gargadi ɓarawon tukunyar mahaifiyarsa

Ya kafa hujja da cewa, a lokacin da aka saki Notcoin, akwai wadanda suka rasa damar cin gajiyar tsarin saboda amfani da ‘Autoclicker’.

Dogs zai fashe nan ba da jimawa ba

A halin da ake ciki, jama’a da yawa ne suka saka ido kan yadda za su kwashi garabasa a duniyar kudin intanet yayin da ake shirin fashewar kudin intanet na Dogs.

A jiya 23 ga wata ne wasu suka hade asusunsu na musayar kudin intanet da fasahar hakar Dogs a manhajar Telegram.

Muhammad Rabiu Jibrin, wani mai hakar wadandan kudade ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa, ana hangen alheri game da wannan kudi da zai fito.

Batu daga kamfanin Tapswap

A wani labarin, kamfanin Tapswap ya magantu yayin da yan Najeriya ke samun cikas a kokarin neman sulalla a manhajarsa.

Wannan na zuwa ne yayin da yan kasar ke kokawa kan dakile su da aka yi wurin daddana Tapswap din.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafin X a yau Juma'a 24 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.