Gwamna a Arewa Ya Zama Na Farko da Ya Fara Biyan Sabon Albashin N70,000 a Najeriya

Gwamna a Arewa Ya Zama Na Farko da Ya Fara Biyan Sabon Albashin N70,000 a Najeriya

  • Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya zama na farko da ya fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
  • Ma'aikatan jihar Adamawa sun tabbatar da haka bayan karɓan albashin watan Agusta, sun kuma yabawa gwamnan
  • A ranar 19 ga watan Agusta, Gwamna Fintiri ya yi alƙawarin cewa ma'aikatan jiha za su fara cin moriyar mafi ƙarancin albashi a ƙarshen wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Gwamnatin Adamawa da ke Arewa maso Gabas ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya ɗauka a makon jiya cewa zai fara biyan ma'aikata sabon albashin a ƙarshen watan Agusta.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi abin da ya hana shi biyan N70,000 bayan Fintiri ya biya ma'aikata

Gwamna Ahmadu Fintiri.
Adamawa: An fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi a watan Agusta Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Twitter

N70,000: Gwamna ya yi alƙawari a Agusta

Tribune Online ta ce shugaban NLC na jihar, Kwamared Emmanuel Fashe ne ya sanar da haka jim kadan bayan ganawa da gwamnan ranar 29 ga Agusta, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ma’aikatan gwamnatin jiha za su fara karɓan albashi tare da ƙarin da ya kamata su samu saboda sabon mafi karancin albashi daga watan Agustan 2024.

Emmanuel ya ƙara da cewa su kuma ma'aikatan kananan hukumomi za su fara cin gajiyar sabon albashin N70,000 a watan Satumba a jihar Adamawa.

Ma'aikata sun fara ganin ƙarin albashi

Ma'aikatan ɓangarori daban-daban a jihar Adamawa sun tabbatar da lamarin bayan karban albashinsu na watan Agusta.

A hira daban-daban, ma'aikata sun yabawa mai girma Gwamna Ahmadu Fintiri bisa halin dattakon da ƴa nuna wajen cika alƙawarin da ya ɗauka.

Wata ma'aikaciya a ma'aikatar filaye da binciken ƙasa, Saliyatu Mohammad ta bayyana gamsuwarta, ta ce gwamna ya nuna yana son walwalar ma'aikata.

Kara karanta wannan

Wasu ƴan Arewa sun yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir, sun aika saƙo ga gwamnoni

Haka zalika wani malamin makaranta, Emmanuel Amos Tumba, ya tabbatar da ƙarin albashin, inda ya ce:

“Ina tabbatar muku da cewa an yi karin albashin kuma na karbi nawa. Ina ƙara yaba wa gwamna kan hakan.”

Bugu da ƙari, wani ma'aikacin gwamnatin jihar Adamawa, Malam Tahir ya tabbatar da haka ga wakilin Legit.ng Hausa ta wayar tarho.

Ya ce kamar yadda gwamnatin Adamawa ta faɗa, ta yi amfani ne da tsarin biyan albashi na 2019 gabanin gwamnatin tarayya ta gama aiki kan sabon tsarin da za a tafi a kai.

"Eh tabbas jiya aka biya albashi kuma indai karkashin jiha kake ka samu ƙari, mun ji daɗi kuma muna murna da hakan. Amma dai ƙananan ma'aikata ne za su fi amfana.
"Misali malaman firamare, wanda ake biya N52,000 a yanzu ya samu N110,000 zuwa N120,000, ka ga su za su fi amfana, amma manyan ma'aikata za ka ga ɗan ƙarin ba wani abu ba ne," in ji Tahir.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanar da sabon tsarin albashi ga ma'aikatan jiharsa? Gaskiya ta fito

Da wannan karimcin jihar Adamawa ta zama jiha ta farko da ta fara biyan mafi karancin albashi na N70,000 tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kai.

Gwamna Fintiri ya hana hadimai fita

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ya dauki matakin hana hadimansa na siyasa fita wajen jihar idan gwamnati ce za ta dauki nauyi.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Humawashi Wounosikou ya rabawa manema labarai a Yola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262