A Karon Farko Bayan Fara Rikicin Sarauta, Sarki na 15 Aminu Ado Ya Fita Daga Kano

A Karon Farko Bayan Fara Rikicin Sarauta, Sarki na 15 Aminu Ado Ya Fita Daga Kano

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tafiya zuwa babban birnin tarayya Abuja domin halartar wani taro da ya kunshi sarakuna
  • Wannan ne karo na farko da Aminu ya fita daga birnin Kano tun bayan ɓarkewar rikicin sarauta tsakaninnsa da Muhammadu Sanusi II
  • A halin yanzu dai babu sarki ko ɗaya a kwaryar birnin Kano sakamakon Sanusi II ya tafi ƙasar Ingila inda ya karisa karatun digiri na uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - A karon farko bayan ɓarkewar rikicin sarauta, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi tafiya zuwa wajen jihar Kano.

Basaraken wanda ya koma Kano a watan Mayu, 2024 bayan an sauke shi daga sarauta, ya fita daga jihar zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan Sarkin Gobir ya harzuƙa Gwamnatin Tinubu, minista ya ba sojoji umarnin gaggawa

Sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
A karon farko bayan fara rikicin sarauta, Aminu Ado Bayero ya yi tafiya zuwa Abuja Hoto: Aminu Ado Bayero
Asali: Facebook

Menene ya kai Sarki Aminu Ado Abuja?

Wata majiya ta ce sarkin ya tafi wata ziyarar aiki ne zuwa Abuja domin halartar wani babban taro da aka gayyaci sarakuna, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba Aminu Bayero ya koma Kano kwanaki kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige shi, kuma tun a wancan lokaci yake ikirarin sarautar Kano.

Aminu Ado ya ci gaba da zama a fadar Nasarawa yayin da Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II ke zama a fadar Ƙofar Kudu bayan mayar da shi kan sarauta.

Tun bayan fara rikicin sarautar, Aminu Ado ya fita daga ƙaramar fadar Nasarawa a karon farko ranar 20 ga watan Yuli lokacin da ya halarci taron saukar Alƙur'ani a Masallacin Isyaku Rabiu.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya tafi Ingila

Kara karanta wannan

'An zalunci yan bindiga,' Sheikh Gumi ya yi magana bayan kisan sarkin Gobir

A halin yanzu, babu sarki a kwaryar birnin Kano sakamakon shi kansa Sanusi na II ya kasar Ingila inda ya ƙare karatun digirin digirgir.

Kazalika an ga Aminu Ado Bayero a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja tare da Oni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, da dai sauransu.

Gwamna Abba zai gina birane a Kano

A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta dauki haramar gina birane kamar yadda ake yi a wasu ƙasashe.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara ƙoƙarin biyan kudi ga wadanda za a yi amfani da filayensu wajen gina biranen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262