Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar shugabar alkalan Najeriya (CJN) ta 23
  • An ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya jagoranci bikin rantsarwar ne a fadar gwamnati da ke Abuja a safiyar Juma’a, 23 ga watan Agusta
  • Mai shari’a Kekere-Ekun za ta kasance a matsayin mukaddashiyar CJN har zuwa lokacin da za majalisar dattawa za ta tabbatar da ita

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin babbar jojin Najeriya (CJN) ta 23 a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kekere-Ekun za ta yi aiki a matsayin mukaddashiya har sai majalisar dattawa ta amince da nadin ta.

Kara karanta wannan

Kogi: Kotun Koli ta yi hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan APC, ta jero dalilai

An rantsar da Mai shari'a Kekere-Ekun matsayin shugabar alkalan Najeriya ta 23
Najeriya ta samu sabuwar shugabar alkalai. Hoto: @officialABAT, @ataweweattorney
Asali: Twitter

Tinubu ya rantsar da Kekere-Ekun

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya rantsar da Kekere-Ekun ne da misalin karfe 11:38 na safe a zauren majalisar zartarwar ta tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya dawo kasar da sanyin safiyar yau Juma’a daga Faransa, ya jagoranci zaman majalisar zartarwar.

Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, mai shekaru 66 ta zama mace ta biyu da ta hau kujerar shugabar alkalan Najeriya, kamar yadda rahoton NTA ya nuna.

Daga Kotun Koli zuwa shugabar alkalai

An ce Mai shari'a Kekere-Ekun ta gaji Mai shari'a Olukayode Ariwoola wanda ya yi ritaya daga mukamin a jiya Alhamis bayan shafe shekaru biyu.

Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta bayar da shawarar a nada Mai shari’a Kekere-Ekun, wanda ta kasance ta biyu mafi daraja a alkalan kotun koli a matsayin shugabar alkalai.

Kara karanta wannan

Kekere Ekun: Abubuwa 4 da muka sani game da sabuwar shugabar alkalan Najeriya

Mai shari’a Kekere-Ekun ta samu daukaka zuwa kotun kolin Najeriya a matsayin mace ta biyar da ta zama alkaliya a kotun kuma an rantsar da ita a watan Yulin 2013.

Abubuwa 4 game da Kekere-Ekun

A wani labarin, kun ji cewa bayanai da dama game da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, sabuwar shugabar alkalan Najeriya na ta fitowa tun bayan rantsar da ita.

Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, wadda ta zama babbar jojin Najeriya ta 23.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.