Ana Shirin Rufe Jami’o’i, Ministan Tinubu Ya Sanya Lokacin Haduwa da ASUU

Ana Shirin Rufe Jami’o’i, Ministan Tinubu Ya Sanya Lokacin Haduwa da ASUU

  • Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya ce gwamnati ta shirya ganawa da kungiyar malaman jami’o’i a ranar Litinin mai zuwa
  • A cewar Farfesa Tahir Mamman, tattaunawar za ta mayar da hankali ne wajen duba bukatun ASUU da yadda za a cimma matsaya
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin ta karbi sakon ASUU na cewa za ta rufe dukkanin jami'o'in kasar a wani mataki na yajin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanya ranar haduwa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) domin magance bukatun malaman.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne yayin da kungiyar ASUU ta ba ta sanarwar tsunduma yajin aiki a cikin kwanaki 21.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta dauki barazanar ASUU da gaske, ta na neman hana yajin aiki

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan shirin shiga yajin aikin ASUU
Ministan ilimi, Farfesa Mamman ya ce za su gana da ASUU ranar Litinin. Hoto: Tahir Mamman, ASUU
Asali: Facebook

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, a wani shirin talabijin da TVC ta ruwaito ya ce gwamnatin za ta gana da ASUU domin duba bukatun malaman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ASUU za ta shiga yajin aiki?

A sakon da malaman jami'o'in suka aikawa gwamnatin tarayya, mun ruwaito cewa ASUU ta ce ba wai gargadi ba ne, sanarwa ce kawai domin kiyaye doka.

Kungiyar ta ce za ta rufe jami'o'in kasar kwanaki 21 daga ranar da ta fitar da sanarwar, saboda gazawar gwamnati na cika alkawurran da ta dauka.

Malaman jami'ar sun zargi gwamnati da yin biris da jarjejeniyar da suka cimmawa a 2009, wanda ta ce hakan ya nuna gwamnati ba ta damu da ilimin manyan makarantu ba.

Ministan Tinubu ya sanya lokaci

A cikin shirin, ministan ilimi ya tabbatar da cewa gwamnati ta samu sanarwar yajin aikin daga shugabannin ASUU kuma gwamnati na kokarin hana yajin aikin.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nemi hakkin 'yan kasa, ya bukaci bayanan sabon jirgin Tinubu

A cewar Farfesa Mamman, ganawar ta ranar Litinin za ta duba bukatun ASUU tare da fitar da hanyoyin da za a bi domin kaucewa wani mataki na shiga yajin aikin.

Ministan ya ce:

“Mun samu takardar sanarwar yajin aikin daga ASUU a ranar Litinin. Mun riga mun tattauna kan bukatunsu, kuma mun tsayar da lokacin haduwa da ASUU domin maslaha."

Kalli tattaunawar a nan kasa:

Minista ya daukarwa ASUU alkawari

A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya ba kungiyar malaman jami'o'i tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace kan bukatunsu.

Farfesa Mamman ya nuna cewa gwamnati ta dauki wasu matakai tun a baya da suka inganta walwalar malaman jami'a, kuma za su yi kokarin hana ASUU shiga yajin aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.