Majalisa Ta Gano Inda Tallafin Buhunan Shinkafar Tinubu Ke Maƙalewa

Majalisa Ta Gano Inda Tallafin Buhunan Shinkafar Tinubu Ke Maƙalewa

  • Majalisar kasar nan ta bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na kokarin raba tallafi domin rage radadin matsin rayuwa
  • Mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ne ya bayyana haka, amma ya ce wasu daidaikun jama'a ne ke dakile kokarin
  • Sanata Barau ya kara da cewa sun gano wasu daga cikin wadanda ake dorawa alhakin raba tallafin na karkatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta bayyana takaicin yadda wasu yan kasar nan ke dakile yunkurin gwamnatin tarayya wajen tallafawa 'yan kasa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya ce gwamnati ta na iya kokarin tallafawa talakawa, amma daidaikun mutane su na hana ruwa gudu.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kare shirinta na gwajin kwaya ga dalibai, za a dauki mataki kan wasu

Barau
Majalisa ta zargi masu hakkin rana tallafin gwamnati da rashin gaskiya Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau ya ce wadanda ake dorawa alhakin raba tallafin na tafka rashin gaskiya ta hanyar karkatar da kayan da aka ba su, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa zuwa yanzu, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince da fara shirye-shiryen tallafi da dama ga talakawan kasar nan da ke fama da yunwa.

"Za a raba shinkafa a Kano" - Barau

Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin ya ce shugaban kasa, Tinubu ya kafa kwamitin da zai tabbatar da rabon shinkafa ga talakawan Kano.

Za a raba shinkafa mai girman 25kg ga mutane 23,644 daga cikin bil adama akalla 15,462,200 da ke zaune a jihar, Premium Times ta wallafa.

Kano: Yadda za a raba tallafin Tinubu

Mataimakin shugaban majalisa, Barau Jibrin ya ce an samar da wasu hanyoyin raba tallafi domin ganin ya karasa inda ake bukata.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nemi hakkin 'yan kasa, ya bukaci bayanan sabon jirgin Tinubu

Daga cikin hanyoyin da ya lissafa akwai amfani da katin shaidar dan kasa, katin zabe, lasisin tuki ko kuma fasfo.

Tinubu ya tura tallafin shinkafa Kano

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta aika da tallafin kayan masarufi ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf domin rabawa ga mabukata a Kano.

Kayan abincin mai yawan tan 2,706, tallafi ne da za a raba ga mazauna jihar a kananan hukumomi 44 domin rage radadin yunwa da ta addabe su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.