Sarkin Gobir: Ƴan Arewa Sun Fusata, Sun Kawo Hanyoyin Maganin Yan Bindiga
- Al'ummar Arewacin Najeriya sun ƙadu kan kisan gillar da masu garkuwa da mutane suka yiwa mai martaba Sarkin Gobir
- Mutane da dama a Arewacin Najeriya sun yi maganganu cikin fushi da suka nuna rai ya yi mugun ɓaci kan kisan Isa Muhammad Bawa
- Legit ta tattauna da wani matashi mai suna Abdullahi Yakubu domin jin ko yana da wani mataki da za a dauka domin maganin yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Al'ummar Arewacin Najeriya sun nuna damuwa kan kisan gillar da yan bindiga suka yi wa sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.
Wasu daga cikin yan Arewa sun fadi hanyoyin da suke gani idan aka bi za a iya maganin yan bindiga a yankin.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu daga cikin maganganun da yan Arewa suka yi a kafafen sada zumunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A fito a yaki yan bindiga"
Wani Abdullahi A. Abdullahi ya wallafa a Facebook cewa ya kamata a fito a yaki yan bindigar saboda kashe sarkin Gobir da hana gawarsa da suka yi.
Ya bayyana cewa ya kamata a samu matasa kamar 100,000 su tunkari maboyar yan ta'addar domin su gama da su.
"A daina biyan kudin fansa"
Nasir Hassan Wagini ya wallafa a Facebook cewa ya kamata al'ummar Arewa su daina biyan kudin fansa ko waye aka kama.
Malam Nasir ya kara sa cewa ya kamata kowa ya zama kamar soja ta yadda ba zai yarda yan bindiga su kama shi cikin sauki ba sai an yi artabu, ko a mutu ko a yi rai.
"Kisan ya yi muni sosai" - Jafar Jafar
Jafar Jafar ya nuna takaici kan yadda yan bindiga suka aikata ta'addanci a kan babban mutum kamar sarkin Gobir.
Dan jaridar ya wallafa a Facebook cewa bai tunanin a wannan karni da muke ciki akwai wani basarake da aka taba yi wa kisan wulakanci kamar sarkin Gobir ba.
Legit ta tattauna da Abdullahi Yakubu
Wani matashi mai suna Abdullahi Yakubu ya zantawa Legit cewa maganar samar da matasa da za su tunkari yan bindiga ita ce mafita.
Abdullahi Yakubu ya ce babu dalilin da za a bar mutane kadan suna yin kisan wulakanci ga al'umma kuma a zuba musu ido.
Matashin ya ce ya kamata a kowane gari a samu matasa da za su sadaukar da ransu domin yakar yan bindiga.
An kama mai garkuwa da mutane
A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suke fitowa daga jihar Filato sun nuna cewa al'umma sun cire tsoro sun kama wani mai garkuwa da mutane da ya sace yara biyu.
Mai garkuwa da mutanen da ake zargi ya karbi kudi a wajen yan uwan wadanda ya sace amma duk da haka bai sake yara biyun ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng