Zamfara: Ana Makokin Sarkin Gobir, Miyagu Sun Kwashe Mutane, An Nemi Fansar N50m

Zamfara: Ana Makokin Sarkin Gobir, Miyagu Sun Kwashe Mutane, An Nemi Fansar N50m

  • Mazauna Arewacin kasar nan sun fada kunci bayan kamari da ayyukan da miyagu su ka yi, musamman a kwanan nan
  • Ana tsaka da jimanin kisan Sarkin Gobir, Mai Martaba Isa Bawa sai labarin sace wasu mazauna jihar Zamfara ya bulla a yau
  • Yan ta'adda sun sace mutane 10 daga yankin Moriki, inda su ka bukaci fansar Naira Miliyan 50, yan sanda sun tabbatar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Mazauna yankin Moriki a jihar Zamfara sun shiga tashin hankali bayan yan ta'adda sun kai masu samame a daren Laraba, tare da sace mutane 10.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun fusata, sun yi tofin Allah tsine kan kisan Sarkin Gobir

Yan ta'addan da su ka yi awon gaba da mutanen da su ka sace, sun bukaci kudin fansa na Naira Miliyan 50.

Zamfara
Miyagu sun kwashe mutum 10 a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

BBC Hausa ta tattaro cewa mazauna yankin sun zargi yan bindigar da kai masu harin ramuwar gayya bisa zargin cewa su ne su ka kashe shanun miyagun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa yan ta'addan sun rika bi gida-gida su na kwashe wanda su ka dama, sannan sun ba su wa'adin da ake son su biya kudin.

Miyagu sun dade su na harin Zamfara

Mazauna yankin Moriki a jihar Zamfara sun bayyana cewa dama yan bindiga sun dade su na kai masu hari a duk lokacin da ta raya masu.

Vanguard News ta tattaro cewa ko a kwanakin baya, sai da miyagun su ka karbi Naira Miliyan 20 daga mazauna yankin kafin su bar su shiga gonakinsu.

Kara karanta wannan

Iyayen marayu, mata sun tsunduma zanga zanga, sun fadi yadda su ke rayuwa a Ondo

Martanin rundunar yan sandan Zamfara

Rundunar yan sanda Zamfara ta tabbatar da harin da miyagu su ka kai yankin Moriki tare da sace mazauna yankin guda 10.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Yazid Abubakar ya ce tuni kwamishinan yan sanda ya bayar da umarnin bin sawun barayin.

Miyagu sun kashe Sarkin Gobir

A wani labarin kun ji cewa miyagu sun kashe Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa duk da shirin da ake na kai masu kudin fansar N60m da su ka nema.

Tuni aka yi jana'izar Sarkin wanda daruruwan musulmai su ka halarta, duk da cewa miyagun sun hana makusantan Sarkin daukar gawarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.