Zanga Zanga Ta Barke kan Kisan Sarkin Gobir, Bayanai Sun Fito

Zanga Zanga Ta Barke kan Kisan Sarkin Gobir, Bayanai Sun Fito

  • Fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a garin Sabon Birni na jihar Sokoto kan kisan da ƴan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir
  • Matasan sun yi ƙone-ƙone a kan tituna bayan sun fusata sakamakon hallaka Alhaji Isa Muhammad Bawa da ƴan bindigan suka yi
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta samu nasarar shawo kan lamarin bayan ta tura jami'an tsaro zuwa garin yayin da ake makoki a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - An gudanar da zanga-zanga kan nisan da ƴan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a jihar Sokoto.

A yayin zanga-zangar dai an yi ƙone-ƙone a kan tituna domin nuna adawa da kisan gillar da ƴan bindigan suka yiwa basaraken.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan bindiga suka karɓi kuɗin fansa sama da N50m duk da kashe Sarkin Gobir

An yi zanga zanga kan kisan Sarkin Gobir a Sokoto
Matasa sun yi zanga-zanga kan kisan Sarkin Gobir a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An yi zanga-zanga kan kisan Sarkin Gobir

Jaridar Aminiya ta ce bayan Sallar Azahar a ranar Alhamis, fusatattun matasa a Sabon Birni sun fito kan tituna suna ƙone-ƙone domin nuna takaicinsu kan kisan basaraken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan kuwa na zuwa ne kimanin sa’o’i uku bayan an gudanar da Sallar Jana’izar marigayin ba tare da gawarsa ba a fadarsa da ke Sabon Birni.

Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir sun hallaka shi tare da binne gawarsa jim kaɗan bayan cikar wa’adin da suka bayar na kai musu kuɗin fansa.

Jikan Sarkin Gobir da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su tare, ya bayyana cewa a ranar Litinin ne ƴan bindigan suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufai, kan lamarin wanda ya tabbatar da aukuwar zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan sarkin Gobir, 'yan bindiga sun sace matar basarake da 'ya'yansa 2

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa sun shawo kan lamarin kafin abubuwa su rincaɓe.

"Dama mun tura tawagar jami'an tsaro zuwa garin. Ko da aka fara zanga-zangar mun samu nasarar shawo kanta. Yanzu komai ya lafa."

- ASP Ahmad Rufai

Atiku ya magantu kan kisan Sarkin Gobir

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan kisan gillar da ƴan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.

Atiku wanda ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan kisan ya ce sakacin gwamnati na rashin nuna damuwa da ɗaukar matakai ya ta'azzara matsalar tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng