Babban Lauya Femi Falana Ya Bankado Adadin Masu Zanga Zanga da Ke Tsare

Babban Lauya Femi Falana Ya Bankado Adadin Masu Zanga Zanga da Ke Tsare

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta kama masu zanga-zanga sama da 2,000 daga jihohin kasar nan daban-daban kwanaki
  • Yan Najeriya sun gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin Bola Tinubu daga 1 - 10 Agusta, 2024 saboda matsin rayuwa
  • Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya zargi jami'an tsaro da kama sama da mutane, ya ce an aika wasu kurkuku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya bukaci rundunar yan sandan kasar nan ta gurfanar da masu zanga-zanga da ta kama kotu.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Fitaccen lauyan ya bayyana haka ne bayan zargin rundunar da cafke masu zanga-zanga kimanin 2,111 daga jihohin kasar nan da aka yi zanga-zanga.

Police
Lauya Femi Falana ya zargi yan sanda da tsare masu zanga-zanga ba bisa ka'ida ba Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro Femi Falana SAN ya ce yanzu haka akwai wasu daga cikin wadanda su ka fita zanga-zanga akalla 1403 da ke tsare a gidan yari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban lauyan ya bayyana cigaba da tsare matasan da jami'an tsaro ke yi a matsayin abin da ya sabawa dokar kasa.

Lauya Falana ya gargadi yan sanda

Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya bukaci rundunar yan sandan kasar nan ta gaggauta gurfanar da wadanda ta kama gaban kotu.

Falana SAN ya ba rundunar daga yanzu zuwa 25 Agusta, 2024 da su mika matasan gaban kotu ko su fuskanci matakin shari'a, Daily Post ta wallafa wannan.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Akpabio, Sanatan Kano da sauran manyan da suka yi wa 'yan kasa izgili

Babban lauyan ya kuma zargi rundunar yan sanda da hana masu zanga-zanga da aka kama damar ganawa da lauyoyin da za su iya ba su kariya.

Falana ya magantu kan gayyatar Ajaero

A wani labarin kun ji cewa lauyan kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Femi Falana SAN ya ce shugaban kungiyar, Joe Ajaero ba zai iya zuwa wurin yan sanda ba.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar ta gayyaci Joe Ajaero ya bayyana gabanta ranar Talata bisa zargin ta'addanci da daukar nauyin zanga-zangar kuka da gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.