Jami'an 'Yan Sanda Sun Dakile Hare Haren 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane 30

Jami'an 'Yan Sanda Sun Dakile Hare Haren 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane 30

  • Rundunar ƴan sanda ta reshen Katsina ta samu nasarar daƙile hare-haren ƴan bindiga a wurare daban-daban na jihar
  • Jami'an rundunar sun kuɓutar da mutane 30 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su a ƙauyukan ƙananan hukumomi uku
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis, 22 ga watan Agustan 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kuɓutar da mutane 30 da aka yi garkuwa da su tare da daƙile hare-haren ƴan bindiga da dama a wurare daban-daban a jihar.

Jami’an ƴan sanda sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Dutsinma tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47. 

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan sarkin Gobir, 'yan bindiga sun sace matar basarake da 'ya'yansa 2

'Yan sanda sun ceto mutane a Katsina
'Yan sanda sun dakile hare haren 'yan bindiga a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun ragargaji ƴan bindiga

Ya bayyana cewa jami'an rundunar tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai a ƙaramar hukumar Dutsinma ƙarƙashin jagorancin CSP Bello Abdullahi Gusau ne suka daƙile harin na ƴan bindiga, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Mutanen da aka ceto an sace su ne daga ƙauyukan Farar Ƙasa da Shanga a ƙaramar hukumar Dutsinma. An garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawa. Haka kuma an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 a yayin samamen."

- ASP Abubakar Sadiq Aliyu

Ƴan sanda sun ceto mutane a Katsina

ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ci gaba da bayyana cewa, bayan wani ƙazamin faɗa, jami’an ƴan sanda sun daƙile harin da ƴan bindiga suka kai a Malumfashi da ƙaramar hukumar Jibia.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun hallaka manyan kwamandojin 'yan ta'adda 5 a Borno, an jero sunaye

Ya ce ƴan sandan sun ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su da kuma shanu biyar da aka sace a ƙauyen Yaba da ke ƙaramar hukumar Malumfashi.

A ƙaramar hukumar Jibia, ƴan sandan sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su daga hannun ƴan bindigan da suka kai hari ƙauyukan Jibian Maje, Nasarawa, da kuma Lankwasau.

Ƴan bindiga sun hallaka ɗan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka jami'in ɗan sandan da suka yi garkuwa da shi a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Ƴan bindigan sun sace jami'in ɗan sandan ne a wajen ƙauyen Kampani da ke gundumar Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar Plateau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng