Bayan Tinubu Ya Tsige Shi, EFCC Ta Dauki Mataki kan Tsohon Shugaban NAHCON

Bayan Tinubu Ya Tsige Shi, EFCC Ta Dauki Mataki kan Tsohon Shugaban NAHCON

  • Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayar da belin tsohon shugaban NAHCON da sakatarensa
  • EFCC ta saki Jalal Arabi tare da Abdullahi Kontagora bayan sun cika sharuɗɗan belinsu a hannun hukumar yaki da rashin gaskiyar
  • Hukumar tana binciken mutanen ne kan zargin karkatar da tallafin aikin Hajjin 2024 na N90bn da gwamnatin tarayya ta ba da

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayar da belin tsohon shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Jalal Arabi.

EFCC ta bayar da belin tsohon shugaban na NAHCON ne tare da sakataren hukumar Abdullahi Kontagora.

Kara karanta wannan

N90bn: EFCC ta fadi yadda aka yi binciken sirri wajen bankado badakalar NAHCON

EFCC ta ba da belin Jalal Arabi
EFCC ta ba da belin tsohon shugaban NAHCON Hoto: @nigerianhajjcom
Asali: Twitter

Meyasa EFCC ta tsare tsohon shugaban NAHCON?

EFCC ta tsare Jalal Arabi da Abdullahi Kontagora ne bisa zargin fitar da kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba da kuma karkatar da tallafin N90bn na aikin Hajjin 2024, cewar rahoton jaridar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ba su iya cika sharuɗɗan belinsu ba, wanda hakan ya sanya suka zauna a hannun EFCC har na tsawon kwanaki biyar.

Hukumar EFCC ta bada belin Jalal Arabi

Jaridar The Punch ta ce wata majiya mai tushe a ranar Laraba ta bayyana cewa Jalal Arabi da Abdullahi Kontagora sun cika sharuɗɗan belinsu.

Majiyar ta ce an sake su ne a ranar Litinin inda ta ƙara da cewa har yanzu ba a ƙara ƙwato wasu kuɗaɗen ba bayan Riyal 314,098 da aka ƙwato tun daga farko.

"An saki tsohon shugaban hukumar Alhazai tare da sakataren hukumar, kuma ana ci gaba da bincike. An sake su ranar Litinin bayan sun cika sharuddan belinsu."

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

"Har yanzu babu wani abu kan lamarin. Babu wani abin da aka sake ƙwatowa bayan abin da aka ƙwato tun da farko."

- Wata majiya

Me EFCC ta ce kan lamarin?

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, kan lamarin ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Dele Oyewale bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba kan lamarin.

Tinubu ya naɗa sabon shugaban NAHCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan) a matsayin Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON).

Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar ta sauke Jalal Ahmad Arabi daga matsayin shugaban NAHCON kan badaƙalar tallafin hajjin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng