Gwamnati Ta Dauki Barazanar ASUU da Gaske, Ta na Neman Hana Yajin Aiki

Gwamnati Ta Dauki Barazanar ASUU da Gaske, Ta na Neman Hana Yajin Aiki

  • Gwamnatin tarayya ta sha alwashin tabbatar da cewa malaman manyan makarantun kasar nan ba su shiga yajin aiki ba
  • Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU), ta yi barazanar tsunduma yajin aiki domin nuna rashin amincewa da halin da suke ciki
  • Duk da ganawa da Ministan Ilimi, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce nan da makonni uku za su shiga yajin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta yi duk abin da ya dace wajen hana kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) tsunduma yajin aiki.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka bayan kammala ganawa da shugabannin kungiyar ASUU a baya domin sake duba bukatunsu.

Kara karanta wannan

Tanka makare da gas ta fadi a Legas, an shiga aikin ceto domin kare rayuka

Kungiyar ASUU
Gwamnati ta fara kokarin shawo kan yunkurin yajin aikin ASUU Hoto: Academic Staff Union of Universities/Hon. Minister of Education, Prof. Tahir Mamman SAN
Asali: Facebook

Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar ilmi, Folashade Biriowo ya ce ministan ya kuma ba shugabannin ASUU tabbatacin duba yiyuwar magance dalilan yajin aiki, Punch ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yanzu haka an dauki wasu matakai da za su kwantarwa ASUU hankali domin ganin ba ta kira yajin aiki a jami'o'in kasar nan ba.

Kungiyar ASUU na shirin yajin aiki?

Kungiyar jami'o'in kasar nan (ASUU) ya bayyana cewa ta sanar da gwamnatin tarayya cewa nan da mako uku za ta tsunduma yajin aiki.

Legit ta wallafa cewa shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana matsayarsu, inda ya ce sun zauna da gwamna a watan Yuni amma har yanzu shiru.

Daga cikin bukatun da ASUU ke da su akwai biyan albashin malamanta da su ke bin gwamnati, dakatar da cire wani kaso na albashinsu da bayar da kudin gyara jami'o'in.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kare shirinta na gwajin kwaya ga dalibai, za a dauki mataki kan wasu

ASUU za ta tsunduma yajin aiki

A wani labarin kun ji cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta gargadi gwamnatin tarayya kan shirinta na tsunduma yajin aiki bisa biris da aka yi da su.

Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka, inda ya ce za su fara yajin aikin nan da kwanaki 21, kuma ba wa'adi su ka ba wa gwamnati ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.