Gwamma Ya Dura kan Ƴan Bindiga, Ya Turmushe Wuraren da Suke Garkuwa da Mutane

Gwamma Ya Dura kan Ƴan Bindiga, Ya Turmushe Wuraren da Suke Garkuwa da Mutane

  • Gwammatin jihar Enugu ta rusa wasu gidaje da ake zargin masu garkuwa na ajiye mutanen da suka sato a wasu sassan jihar
  • Shugaban hukumar raya babban birnin Enugu, Uche Anya ya ce sun kwato makamai da suka haɗa da bindigun AK-47
  • Ya ce Gwamna Peter Mbah ne ya ba da umarnin rusa irin waɗannan gine-gine kamar yadda dokar jihar Enugu ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Gwamnatin Enugu karkashin jagorancin Peter Mbah ta rushe wasu gine-gine da ake zargin masu garkuwa na ɓoye mutanen da suka sato.

Wannan mataki na zuwa sa'o'i ƙalilan bayan jami'an tsaro sun hallaka miyagu 27 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamnatin Kaduna ta bullo da matakin ceton mazauna kananan hukumomi 7

Gwamnan Enugu Peter Mbah.
Gwamnatin Enugu ta rusa maboyar masu garkuwa, an kwato makamai Hoto: Mr Peter Mbah
Asali: Twitter

Shugaban hukumar raya babban birnin Enugu, Uche Anya ne ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati wajen rushe kangwayen gidajen, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an gwamnati sun yi wannan rusau ne a wasu yankuna da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Enugu ta Gabas.

Yadda aka rusa maɓoyar ƴan bindiga a Enugu

Haka nan kuma gwamnatin ta rusa wani bene mai hawa uku wanda ba a kammala ba tare da ramin karkashin kasa a Nkwubor Layout da ke Emene-Nike.

"Miyagun ayyukan da suke aikatawa suna da ban tsoro, kuna ganin yadda suka haɗa tantuna a ƙarƙashin ƙasa, a haka zaka yi tunanin ba komai a wurin.
"Jami'an tsaro ne suka iya gano akwai ramin da ake ajiye mutane a karƙashin ƙasa, mun gano makamai har da bindigun AK-47 da dai makamai da haramun ne farar hula ya mallaka.

Kara karanta wannan

Mutum 2 ƴan gida sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa da su a Arewa

"Amma a yau mun rusa wurin bisa umarnin mai girma gwamna kamar yadda dokokin jihar Enugu suka tanada," in ji Mista Anya.

Wasu kadarorin da gwamnatin ta ruguje sun haɗa da wani katafaren gidan gona da ke dauke da kaji, da alade, da kuma gonaki a Ogbeke-Nike.

Gwamnatin Enugu ta kwato makamai

Mista Anya ya ce gwamnatin jihar ta kwato wasu makamai da alburusai daga maboyar masu garkuwa da aka rusa, rahoton Ripple Nigeria.

Shugaban hukumar ya ce a Emene Nike sun kwato bindigogi 17, da suka hada da bindigogin AK-47 guda takwas, bindigogin fanfo guda bakwai da wasu bindigu biyu.

Gwamnan Zamfara ya naɗa wanda ake zargi?

A wani rahoton kuma Gwamnan Zamfara ya musanta naɗa wanda ake zargi da ayyukan ta'addanci a matsayin mai ba da shawara ta musamman.

Ya ce takardar naɗin da ke yawo da ake tunanin daga gwamnatinsa ta fito ba gaskiya ba ne, zancen nada Bashir Hadeija karya ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262