Bayan Kisan Sarkin Gobir, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Yunkurin Kubutar da Likitar da aka Sace

Bayan Kisan Sarkin Gobir, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Yunkurin Kubutar da Likitar da aka Sace

  • Gwamnatin tarayya ta fara ƙoƙari domin kubutar da likitar da aka sace a jihar Kaduna, Dakta Ganiyat Papoola daga hannun yan bindiga
  • Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya rubuta takarda ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu
  • Haka zalika Farfesa Pate ya mika korafi ga sufeton yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun kan ganin an kubutar da Ganiyat Papoola

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnatin tarayya ta fara ƙoƙarin ƙubutar da wata likita mai suna Dakta Ganiyat Papoola da ta shafe kusan watanni takwas a hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni na nuni da cewa ministan lafiya na kasa, Farfesa Muhammad Pate ya tura sako ga jami'an tsaro da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a kan likitar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani kan marigayi Sarkin Gobir da masarautarsa

Kaduna
Gwamnati ta bukaci kubutar da likita a Kaduna. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa yan bindigar sun sake mijin likitar tun ranar 8 ga watan Maris amma sun cigaba da riketa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin likitar na raye?

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar na cigaba da kiran yan uwan Dakta Ganiyat Papoola domin su tabbatar tana nan da ranta.

Sai dai tun ranar 24 ga watan Yuli da aka yi magana da ita ba a kara jin muryar Dakta Ganiyat Papoola ba.

Sakon Minista zuwa Nuhu Ribadu

Ministan lafiya na kasa, Farfesa Muhammad Pate ya tura bukatar kubutar da Dakta Ganiyat ga Malam Nuhu Ribadu.

Ma'aikatar lafiya ta bayyanawa Nuhu Ribadu cewa tana bukatar gudunmawarsa wajen ganin likatar ta ƙubuta.

Ana so 'yan sanda su ceto likita

Haka zalika Farfesa Muhammad Pate ya tura sako ga sufeton yan sanda kan kubutar da Dakta Ganiyat Papoola.

Kara karanta wannan

"Ba zai iya ba," Malami ya buƙaci Shugaba Tinubu ya tsige Minista 1 nan take

Sahara Reporters ta wallafa cewa kungiyar likitoci ta yi barazanar shiga yajin aiki matukar ba a ƙubutar da likitar ba a ranar 26 ga Agusta.

Sojoji sun gwabza da miyagu a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa an yi artabu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a garin Gudiri da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar Filato.

Rahotanni sun ce an kashe ‘yan bindiga da dama da kuma wasu sojoji yayin artabun da suka yi a kokarin sojojin na yaki da ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng