Dattijo a Najeriya, Tanko Yakasai Ya Tsame Kansa daga Kirkiro Wata Tafiyar Arewa
- Dattijo a Arewacin kasar nan, Alhaji Tanko Yakasai ya ce ba shi da masaniya a kan sabuwar kungiyar siyasa da aka kirkira
- An samu rahotannin samar da wata kugiya mai suna The League of Northern Democrats, wacce aka ce har da shi a cikinta
- Da yake karin haske, ya ce an yi kuskuren wallafa sunansa a matsayin daya daga cikin wadanda ke cikin sabuwar tafiyar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Dattijo a Arewacin kasar nan, Alhaji Tanko Yakasai ya nesanta kansa daga sabuwar kungiya ta The League of Northern Democrats.
Alhaji Tanko Yakasai ya kara da cewa an yi kuskure a rahoton da ya sanya sunansa daga cikin masu tafiyar, kuma wadanda su ka kafa kungiyar.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa dattijon ya kara da cewa jama'a da dama sun kira shi kan batun sabuwar kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya bayyana matsayarsa ne biyo bayan kiraye-kirayen da ya rika samu daga masoyansa da sauran jama'a.
Dattijo Yakasai ya barranta da sabuwar kungiya
Daya daga cikin wadanda su ka kafa kungiyar ACF, Alhaji Tanko Yakasai ya nemi jama'a su yi watsi da rahoton da ya ce an kirkiro wata sabuwar kungiya da shi.
Jaridar Punch ce ta wallafa labarin da ke cewa Alhaji Tanko Yakasai da wasu kusoshin Arewa da yan siyasa sun kafa sabuwar kungiya domin farfado da yankin.
A martaninsa, dattijo a Kano, Yakasai ya nemi jama'a kar su gaskata labarin, inda ya ce ba shi da gadinsa sabuwar kungiyar ta The League of Northern Democrats.
Dattijan Arewa sun kafa sabuwar kungiya
A baya mun ruwaito cewa wasu dattijai da 'yan siyasa a Arewacin kasar nan sun samar da sabuwar kungiya ta League of Northern Democrats.
Manyan Arewa sun kirkiri kungiyar da niyyar fargado da siyasa da cigaban yankin, kuma ana shirye-shiryen gudanar da gagarumin taro a Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng