Ana Jimamin Kisan Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Basarake da 'Ya'yansa 2
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a ƙauyen Galadimawa da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da matar basaraken ƙauyen tare da ƴaƴansa guda biyu a yayin harin
- Ƴan bindigan waɗanda suka je da niyyar su sace basarsaken ne a harin da suka kai cikin dare sai ba su tarar da shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Galadimawa da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da matar basaraken garin tare da ƴaƴansa guda biyu a yayin harin.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Jaridar Daily Trust ta ambato majiyoyi daga ƙauyen na bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen da ƴan bindigan suka sace sun haɗa da matarsa Fatima Aliyu da ƴaƴansa Abdullahi Aliyu da Kamal Aliyu.
Ƴan bindigan masu yawan gaske sun fara harbe-harbe bayan sun isa ƙauyen domin tsoratar da mutane kafin su fasa katanga domin shiga gidan basaraken.
Sarkin Fadan Galadimawa, Hussaini Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Talata, inda ya nuna matuƙar damuwa.
Ya bayyana cewa an ji maharan suna tambayar inda gidan basaraken yake, wanda hakan ke nuna cewa sun zo ne musamman domin su sace shi amma ba su same shi ba.
Malam Umar ya ci gaba da bayanin cewa ƴan bindigan sun yi ɓarna a gidan ciki har da lalata silin nayan sun haura ta katanga.
Da ba su samu basaraken ba, sai suka yi awon gaba da matarsa ta biyu da ƴaƴansa biyu.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, kan lamarin.
Lokacin da aka kira shi a waya ba a jinsa sosai saboda yana tuƙi ne inda ya buƙaci a tura masa saƙo ta wayarsa.
Sai dai, bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Sojoji sun gwabza faɗa da ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga da dama sun baƙunci lahira a wata musayar wuta da suka yi da sojoji a ƙauyen Gudiri da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Plateau.
Sojoji tare da haɗin guiwar ƴan banga sun kai samame sansanin ƴan bindigar dajin bayan samun bayanan sirri kan yawan hare-hare a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng