Kano: Wani Jirgi Ɗauke da Fasinjoji Ya Gamu da Mummunan Hatsari, An Rasa Rayuka
- Wani kwale-kwale da ya ɗauko mutane sama da 10 ya gamu da hatsari a kauyen Kauran Mata da ke karamar hukumar Madobi a Kano
- Rahotanni sun nuna cewa mutum huɗu daga ciki sun mutu, kana an ceto wasu mutum biyar da ransu kawo yanzu
- Mazauna yankin sun ce wannan shi ne karo na farko da jirgin ruwa ya yi haɗari a kogin, inda ya ɗora laifin kan lodi fiye da ƙima
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mutum huɗu daga kauyen Kauran Mata da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano sun rasu sa'ilin da Kwale-kwalen da suke ciki ya yi haɗari.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ruwan ya ɗauko mutum 16 a lokacin da ya kife ranar Talata da yamma.
Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da wadanɗa haɗarin jirgin ya rutsa da su ke hanyar dawowa daga garin Karfi, karamar hukumar Kura inda suke aikin sarrafa shinkafar gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: An ceto mutum 5 da rai
Zuwa yanzu dai an yi nasarar ceto mutum biyar da ransu ciki har da direban kwale-kealen da wata mata mai goyo amma ɓa a ga ɗan da take goyon ba.
Har yanzun ana ci gaba da laluben sauran fasinjoji shida da hatsarin ya rutsa da su, rahoton PM News.
Jami'in hulɗa da jama'a na gwamnatin ƙaramar hukumar Madobi, Jamilu Mustapha Yakasai ya tabbatar da gano gwarwakin mutum huɗu.
Ya faɗi sunayensu da Maryam Jibrin, Yusuf Galinja, Kabiru Muhammad da Safiyanu Musa, kuma ya ce an yi masu jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada.
Kantoman Madobi ya yi ta'aziyya
Ya ce shugaban riko na karamar hukumar Madobi, Alhaji Muhammad Sani Gora ya ziyarci ƙauyen Kauran Mata domin jajantawa jama’a kan lamarin.
Wani mazaunin Kauran Mata, Salisu Adamu Baure ya ce wannan shi ne karo na farko da irin wannan hatsarin ya afku a kogin, inda ya alakanta lamarin da cika lodi.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kansilan Kauran Mata, Aminu Garba ya kai masu rahoto.
Jirgin sama ya yi haɗari a Brazil
A wani rahoton kuma wani jirgin sama ɗauke da fasinjoji 62 ya yi haɗari a kusa da Sao Paulo a kasar Brazil ranar Jumu'a, 9 ga watan Agusta, 2024
Rahotanni sun bayyana jirgin ya faɗo ne a kusa da wani gida kuma duka mutane 62 da ke ciki sun mutu, shugaban ƙasar ya aika sakon ta'aziyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng